Dakarun soji sun daƙile wani hari da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai wani sansanin soji da ke Buni Yadi, a ƙaramar hukumar Gujba a Jihar Yobe.
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:25 na daren ranar Asabar, inda ‘yan ta’addan suka dinga harbe-harbe.
- Wang Yi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Sabon Ministan Harkokin Wajen Sudan Ta Kudu
- Sin: Matakin Harajin Kwastam Da Amurka Ta Dauka Babakere Ne
Rahotanni sun nuna cewa an kashe wasu daga cikin sojoji da ‘yan ta’addan, sai dai ba a bayyana adadinsu ba.
Wasu mazauna yankin sun ce sojojin sun mayar da martani cikin sauri sannan sun kira ƙarin runduna, wanda hakan ya tilasta wa ‘yan ta’addan tserewa.
Wani soja ya tabbatar da cewa sun kashe ‘yan ta’adda da dama tare da ƙwato motoci biyu da makamai daga hannunsu.
A yayin harin, mutane da dama sun gudu zuwa dazuka, amma sun fara dawowa yayin da zaman lafiya ya fara samuwa.
“Yanzu mutane sun fara dawowa garin kuma abubuwa sun fara dawowa dai-dai,” inji wani mazaunin yankin.
Wani dagacin ƙauyen, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce an samu zaman lafiya kuma al’umma sun fara komawa harkokinsu na yau da kullum.
“Muna gode wa sojojin bisa yadda suka daƙile harin cikin gaggawa,” inji shi.
Wannan ba shi ne karo na farko da aka kai hari a Buni Yadi ba, lamarin da ke ƙara tayar da hankalin jama’a game da buƙatar ƙarin tsaro a yankin.
Mazauna yankin na kira ga gwamnati da ta tura ƙarin sojoji don hana faruwar irin wannan hari a gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp