Sojojin Runduna ta 12 na Rundunar Sojin Nijeriya sun daƙile harin ’yan bindiga kuma sun ceto wani mutum da aka sace, yayin wani samame da suka gudanar a yankin Oshokoshoko da Obajana a ƙaramar hukumar Lokoja a Jihar Kogi.
Kakakin rundunar, Laftanar Hassan Abdullahi, ya ce wannan aiki na cikin ƙoƙarin da sojoji ke yi don yaƙi da ’yan fashi, garkuwa da mutane da sauran laifuka a jihar Kogi.
- Tinubu Ya Umarci A Tsaurara Tsaro A Dazukan Kwara, Neja Da Kebbi
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Tattaunawar Xi Da Trump Tana Da Ma’ana
Ya bayyana cewa da safiyar ranar 25 ga watan Nuwamba 2025, sojoji sun samu sahihan bayanai cewa ’yan bindiga na kan hanyarsu ta Oshokoshoko zuwa Obajana tare da mutanen da suka sace.
Sojojin da ke sansanin Kabba tare da wasu rundunonin haɗin guiwa suka shirya musu kwanton ɓauna.
Da ’yan bindigar suka iso, suka buɗe wa sojoji wuta amma sojojin suka fi ƙarfinsu.
An kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigar, sauran kuma suka gudu da raunukan harbin bindiga.
Sojojin sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47 ɗaya, kuma sun ceto mutum ɗaya da aka sace wanda aka same shi ɗauke da rauni.
An garzaya da shi asibiti domin kulawa.
Laftanar Abdullahi ya ce har yanzu ana ci gaba da neman sauran ’yan ta’addan da suka gudu.
Ya tabbatar da cewa rundunar sojin Nijeriya tana ci gaba da matsa wa miyagu lamba domin kare al’ummar Kogi.














