Sojojin Operation Hadin Kai (OPHK), Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, sun ceto mutane 86 da aka sace tare da kama masu kai wa ‘yan ta’adda kayayyaki su 29 a Jihar Borno.
A cewar Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Haɗin Gwiwa ta OPHK, Laftanar Kanar Sani Uba, sojojin Bataliyar Sojoji ta Musamman ta 135, ƙarƙashin Sashe na 2 OPHK, a ranar 9 ga Nuwamba, 2025, sun yi artabu da ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP a Dutse Kura bayan sun gano cewa ‘yan ta’adda suna sace mutane da motoci a kan hanyar Buratai zuwa Kamuya.
- An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025
- Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL
Uba ya ce, sojojin sun dakile harin, kuma sun fatattaki ‘yan ta’addan zuwa Mangari, wanda ya tilasta wa ‘yan ta’addan tserewa a tarwatse da raunuka.
Ya ƙara da cewa, binciken yankin ya haifar da gano wasu gine-ginen ‘yan ta’adda guda 11 da kuma ceto waɗanda aka sace 86, waɗanda suka haɗa da maza, mata da yara.
A wani samame makamancin haka, sojojin da aka tura Mangada, sun kama masu samar da kayayyaki ga ‘yan ta’adda su 29 a kan hanyar Chilaria dauke da kayayyaki da dama.
Abubuwan da aka kwato daga gare su sun hada da motocin daukar kaya guda biyu da babura masu kafa uku (Keke-napep) dauke da Man fetur, kimanin lita 1,000 a cikin jarkuna, galan hudu na man injin, sabbin tayoyi biyu na motar da ake kafa bindiga, tarin kayan magunguna, da kayan abinci da kayan masarufi.
Uba ya bayyana cewa, an gudanar da hare-haren dukka cikin nasara ba tare da wani soja ya samu rauni ba.














