Ƙasurgumin ɗan bindigar nan da ya addabi jihohin Sakkwato da Zamfara da kuma Katsina, Kachalla Damina, ya baƙunci lahira tare da wasu daga cikin manyan yaransa.
Wannan na zuwa ne biyo bayan artabun da sojojin Nijeriya suka yi da Kacalla tare da yaransa bayan samun wasu bayanan sirri.
- Sojojin Sama Sun Lalata Ma’ajiyar Makaman ‘Yan Ta’adda A Neja
- Tashin Farashin Kayan Abinci Ya Haura Kashi 31.70 A Nijeriya – NBS
Bayan samun bayanan ne rundunar sojin saman Nijeriya suka yi dirar mikiya a kan maharan yayin da suke yunƙurin zuwa ƙauyen Ƙwana da ke Ƙaramar Hukumar Bunguɗu ta Jihar Zamfara a ranar Lahadi.
Dama ƙasurgumin ɗan bindigar na fama da munanan raunukan da ya samu yayin wata arangama da ya yi da rundunar Operation Hadarin Daji a yankin Ɗansadau, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikin yaransa.
Bayanan sirri sun bayyana wa Zagazola Makama cewa kimanin babura 58 ne É—auke da ‘yan ta’addar yayin da suke yunÆ™urin kai hari suka sha luguden wuta, wanda ake kyautata zaton cewa waÉ—anda suka tsira ba za su wuce 11 ba.
A harin dai an hallaka sama da ‘yan ta’adda 50 tare da kuma Æ™one baburansu, a yayin artabun da suka yi da sojin Nijeriya.
Damina ya shahara wajen kashe mutanen da yin garkuwa da mutane da nufin neman kuÉ—in fansa daga iyalansu.