Hedikwatar tsaro a jiya Asabar ta ce dakarun Operation Whirl Stroke sun kai samame a wata masana’antar kera bindiga inda suka kama wasu masu aiki a masana’antar da kuma kwato makamai a jihar Taraba.
Sanarwar da daraktan watsa labarai na tsaro; Manjo Janar Musa Danmadami, ya ce a ranar 28 ga watan Afrilun da ya gabata, sojojin bayan samun sahihan bayanan sirri sun kai samame a wata masana’antar kera makamai a kauyen Wukari da ke karamar hukumar Wukari ta jihar Taraba.
Ya ce sojojin sun kama wasu mutane biyu a masana’antar tare da kwato muggan makamai masu yawa wadanda suka hada da bindigu da alburusai da bama-bamai daban-daban.
Ya ce duk wadanda aka kama da makaman da aka kwato an mika su ga hukumomin da suka dace domin cigaba da bincike.
Babban kwamandan rundunar ya yabawa sojojin na Operation Whirl Stroke tare da yin kira ga jama’a da su baiwa sojojin bayanai masu inganci kuma akan lokaci kan ‘yan ta’adda da duk wasu masu aikata munanan laifuka a yankunansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp