Rundunar sojojin Nijeriya ta kai farmaki yankin Oshodi da ke Legas, ranar Litinin din da ta gabata a kokarinta na kawar da bata-gari.
Sojojin sun tabbatar da cewa, sun kama mutum 116 da ake zargi da aiakata laifuka.
Sannan an samu wasu da bindiga kirar gargajiya, da kuma miyagun kwayoyi da wayoyi wadanda ake zargin cewa satarsu suka yi.
Kwamandan runduna ta 9 Birgediya Janar Isang Akpaumotia, ya ce yankunan da suka kai samamen su ne Railside da Brown da Araromi da kuma wasu a Oshodi.
Janaral din ya bayyana cewa za su binciki dukkan wadanda suka Kaman.
Sannan kuma ya ce dukkan kwayoyin da suka kama za su mika su ga hukumar, NDLEA domin ta yi irin nata aikin.
Sanan kuma Akpomutia ya kara da cewa, rundunar sojojin za ta ci gaba da matsa kaimi wajen yaki da dukkan masu laifi a kowane lungu da sako na yankin.
Shi kuwa mataimakin daraktan mai Magana da yawun rundunar sojojin na Birget ta 9 Mejo A.K. Bello, cewa ya yi suna shirya irin wannan dirar mikiyar ne wuraren da aka aika ta laifuka domin kawo karshen miyagun ayyuka a jahar ta Legas.
Mai magana da yawun eundunar sojojin ya ya tabbatar da cewa, bayan gudanar da bincike, an saki dukkan wadanda aka tabbatar da cewa, ba su da laifi.