Majalisar ÆŠinkin Duniya (MDD) ta yi tir da harin ranar 24 ga watan Janairu da sojojin Nijeriya suka kai kan wasu Fulani makiyaya a Jihar Nasarawa da ke tsakiyar Nijeriya.
BBC Hausa ta rawaito cewa, harin ya yi sanadiyyar kashe mutum aƙalla 40, a cewar MDD.
- Karin Bayani Kan Harin Bom Din Da Ya Kashe Fulani 39 A Nasarawa — Ganau
- Ana Zargin Sojoji Da Kisan Fulani Makiyaya 39 A Nasarawa
Mai bai wa MDD shawara ta musamman kan kare kisan ƙare-dangi, Alice Nderitu, ita ce ta yi wadai da kisan, tana mai bayyana damuwa game da ƙaruwar hare-hare a arewa maso yamma da kuma tsakiyar Najeriyar.
“Irin wannan hare-hare a kan mutane kawai saboda Æ™abilarsu ka iya ta’azzara rikicin Æ™abilanci, da shiga Æ™ungiyoyin ‘yan bindiga, da hare-haren ramuwar gayya, wanda zai dinga Æ™arewa a kan fararen hula,” in ji ta.