Rundunar sojin Nijeriya ta kama sojan da ya kashe wani matashi mai zanga-zangar yunwa a garin Zariya na Jihar Kaduna.
Mai magana da yawun rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya ce sojan ya kashe mai zanga-zangar ne a lokacin da yake kokarin tarwatsa wasu bata gari.
- Gwamnatin Zamfara Ta Ƙaryata Ware Biliyan 19 Don Sanya Wa Lawal Kayan Girki
- CHINADA Ta Nuna Shakku Ga Hukuncin Da Aka Yanke Kan Dan Wasan Tsalle-tsalle Da Guje-guje Na Amurka Game Da Shan Maganin Kara Kuzari
Nwachukwu, ya ce an kama sojan wanda ya yi harbin da nufin gargadin masu zanga-zangar amma ya harsashi ya samu matashin.
Kakakin rundunar ya bayyana cewa dakarun sojin Nijeriya a ranar 6 ga watan Agusta, 2024, sun samu kiran gaggawa cewa “wasu bata gari sun taru a Samaru, suna ƙone tayoyi a kan hanya tare da jifan jami’an tsaro da duwatsu.”
Ya ce nan take sojoji suka suka isa wajen domin tarwatsa gungun matasan tare da tabbatar da dokar hana fita da gwamnatin Jihar Kaduna ta sanya.
“A lokacin da suka isa wajen, bata garin sun yi yunkurin kai wa sojojin hari, lamarin da ya sa wani soja ya yi harbin gargadi don tsoratar da su, amma lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani matashi dan shekara 16 mai suna Ismail Mohammed,” in ji shi.
Nwachukwu ya jaddada cewa “An kama sojan kuma ana yi masa tambayoyi.”
Ya kara da cewa an yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, wanda manyan sojojin Nijeriya suka halarta.