Dakarun rundunar hadin guiwa ta JTF a Tundun Wada sun kama wani mutum wanda aka sakaya sunansa mai shekaru 55 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, a wani samame da jami’an tsaro suka kai a kauyen Sumana da ke cikin karamar hukumar Tundun Wada a jihar Kano.
Kamen wanda ya gudana a ranar 20 ga Afrilu, an bayyana haka ne a wata sanarwa a ranar Talata ta hannun Capt. Babatunde Zubairu, mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta 3 Brigade a Kano.
- Ganduje Ya Soki Buba Galadima, Ya Ce “Ɗan Siyasa Ne Mara Tasiri”
- Gwamnan Edo Ya Dakatar da Sarki Saboda Matsalar Tsaro A Yankinsa
Bayan kama shi, an gurfanar da shi a gaban Kwamanda, Birgediya Janar Ahmed Tukur, wanda ya ziyarci sojoji a sansanin ‘Forward Operating Base (FOB)’ Falgore da ke karamar hukumar Doguwa domin gudanar da bukukuwan Ista (Easter).
Janar Tukur ya yaba wa sojojin bisa jajircewa da kwarewa da suka nuna a yayin aikin, wanda ya kai ga kwato tarin makamai da alburusai da sauran su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp