Sojojin Nijeriya sun yi nasarar kashe wani sanannen ɗan ta’adda tare da kama mutane 22 masu satar shanu a jihohin Kaduna da Filato. An kuma kwato shanu 150 da makamai daban-daban.
A Jihar Kaduna, Sojojin sun kai farmaki a kusa da ƙauyen Gayam a ƙaramar hukumar Birnin Gwari, inda suka kashe wani ƙasurgumin ɗan ta’adda. An kuma kama wasu mutum 18 da ake zargi da kwacen shanu 150. A Jihar Filato kuwa, an kama wasu mutum huɗu bisa laifin satar shanu a Barkin Ladi.
- Sojoji Sun Cafke Masu Safarar Makamai 5 A Filato
- Mun Samu ‘Yan Takara Masu Tu’ammali Da Miyagun Kwayoyi – Hukumar Zaben Kaduna
Haka zalika, a Jihar Borno, Sojojin sun kashe wani ɗan ta’adda, sun kuma ceto wanda aka yi garkuwa da shi tare da kwato wata mota ɗauke da harsasai. Sauran jihohin da aka samu nasara a ayyukan sun haɗa da jihar Ribas, da Enugu, da kuma Binuwai, inda aka kama wasu masu laifin tare da kwayoyi makamai da muggan kwayoyi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp