A ƙalla ƴan bindiga 30 da jami’an tsaro biyar da wani farar hula guda ɗaya ne suka mutu a wani artabu mai zafi da ya gudana a ƙaramar hukumar Faskari, jihar Katsina. Wannan ya biyo bayan hare-haren da ƴan bindiga suka kai wa ƙauyukan Kadisau, da Raudama da Sabon Layi da misalin ƙarfe 5 na yamma a ranar Litinin, 8 ga Yuli, 2025.
Sanarwar ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar ta bayyana cewa rundunar haɗin gwuiwa da ta ƙunshi Sojoji, da ƴansanda, da rundunar Sojin sama ta fatattaki maharan tare da kashe mutum 30 daga cikinsu ta hanyar musayar wuta da luguden wuta daga sama. Duk da nasarar, jami’an tsaron, uku daga rundunar ƴansanda da Sojoji biyu sun mutu, sai kuma wani farar hula daga ƙauyen Kadisau, mai suna Aliyu Sa’adu.
- CMG Za Ta Gabatar Da Labaran Sinawa Na Yakin Kin Harin Sojojin Japan Bisa Fifikonta Na Yayata Labarai A Duniya
- Sin Na Bikin Cika Shekaru 88 Da Dukkan Al’ummar Kasar Ta Fara Yakin Kin Jinin Harin Sojojin Japan
Kwamishinan ma’aikatar, Dr. Nasiru Mua’zu, ya bayyana jimami tare da mika ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin Gwamna Dikko Radda za ta ci gaba da ƙoƙari wajen murƙushe ƴan ta’adda. Ya ce an ƙara zafafa ayyukan tsaro da haɗin gwuiwar hukumomin tsaro na tarayya don dawo da zaman lafiya.
An kuma tabbatar da cewa wani Soja, Ya’u Aliyu, ya jikkata a fafatawar kuma yana karɓar magani. Mua’zu ya shawarci jama’a da su ci gaba da kasancewa masu lura da tsaro tare da isar da bayanai cikin gaggawa ga hukumomin tsaro don tunkarar duk wani barazana.
Gwamnatin jihar ta ce ana ci gaba da bincike kan wannan hari, tare da kiran haɗin kai daga al’umma domin murƙushe barazanar da ke addabar yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp