A ci gaba da aikin share ‘yan ta’adda, rundunar sojoji da ke bataliya ta ‘1 Division’ da ke Kaduna na ci gaba da samun gagarumin nasara inda suka kashe wani dan fashin daji da ceto wadanda aka yi garkuwa da su mutum shida a Hayin Tsando da ke Maraban Jos a jihar Kaduna.Â
A wata sanarwa mai dauke da sanya hannun mai rikon mukamin mataimakin daraktan yada labarai na 1 Division, Liyutanal Kanal Musa Yahaya, ya ce, dakarun sojin sun yi amfani da bayanan sirri kan garkuwa da aka yi da mutane 6 a Hayin Tsando da ke Maraban Jos, cikin gaggawa suka bazama tare da kaddamar da bincike da kokarin ceto wadanda aka sacen.
- Kwarewar Sabon Shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN)
- Zaben Kano: Ba Mu Yarda A Karya ‘Yancin Dimokuradiyya Ba – Kungiya
Liyutanal Konal Yahaya, ya kara da cewa a lokacin samamen, sojoji sun samu nasarar ceto wadanda aka yi garkuwa da su din su shida, tare da kwato bindiga kirar AK-47 guda biyu sannan kuma sun hallaka dan bindiga daya, yayin da sauran suka arce da harbin bindiga a jikinsu.
Ya ce, kwamandan da ke bada umarni (GOC) na 1 Division kuma kwamandan rundunar Whirl Punch, Manjo Janar Valantine Okoro, ya yaba wa dakarun sojin bisa jajircewa da yin aiki tukuru.
Ya kuma bukacesu da su kara himma har sai sun tabbatar dukkanin masu aikata ta’addanci sun daina gabaki daya.
Kazalika, ya roki mutane da cewa duk inda suka ga wani da harbin bindiga a jikinsa da su gaggauta kai rahoton hakan ga sojoji ko kuma sauran bangarorin tsaro da suke kusa da su domin hanzarin daukan matakan da suka dace.