Dakarun rundunar Operation Whirl Punch sun kashe kasurgumin dan ta’addan Buharin Yadi da yaransa da dama a kan iyakar Jihar Kaduna da Katsina.Â
Buharin Yadi ya shafe sama da shekaru goma yana ta’addanci a Arewacin Nijeriya, inda ya jagoranci satar shanu, cinikin makamai, safarar miyagun kwayoyi, da hare-hare da dama.
- Yadda Aka Gudanar Da ‘Tattakin Zaman Lafiya’ A Jihar Zamfara
- Kocin Borrusia Dortmund Edin Terzic Ya Ajiye AikinsaÂ
Dakarun sun kai farmakin ne karkashin jagorancin Manjo Janar MLD Saraso, biyo bayan rahotannin sirri da suka samu, inda aka yi kazamin artabu wanda dakarun suka hallaka akalla ‘yan bindiga 36.
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya yaba wa sojojin tare da bayar da tabbacin ci gaba da bainwa jami’an tsaro goyon baya, yayin da ya bukaci jama’a da su kai rahoton duk wani da ba su yarda da shi ba ga hukuma.