Dakarun Sojin Nijeriya sun kashe wasu ’yan ƙungiyar Boko Haram da ISWAP guda huɗu da ke safarar kayayyaki zuwa ga ’yan ta’adda a Jihar Borno.
An gudanar da aikin ne a ranar 25 ga watan Oktoba, 2025, a ƙaramar hukumar Konduga, a ƙarƙashin Operation Desert Sanity IV.
- APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba
- Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa sojojin sun yi musu kwanton ɓauna a wurare uku; Kuka Uku, Kawuri, da Alou Dam, inda suka kashe masu ɗaukar kayan ’yan ta’addan huɗu.
Rundunar ta tabbatar da cewa babu wanda ya jikkata daga ɓangaren sojoji, kuma waɗanda aka kashe sun kasance mambobin Boko Haram da ISWAP.
An ce aikin na daga cikin ƙoƙarin sojojin na lalata hanyoyin samar da kayayyaki ga ’yan ta’adda da tabbatar da tsaron yankin, kodayake an ce yankin na fuskantar barazana.














