Dakarun sojin Nijeriya sun kashe wasu mayaƙan ISWAP, sun kuma kama mutane 19 da ake zargin suna ’yan ta’ammali da miyagun ƙwayoyi tare da ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su a wasu hare-hare daban-daban a fadin ƙasar nan.
A yayin samamen, an kuma cafke masu tallafa wa ’yan ta’adda, shugabannin masu garkuwa da mutane, ’yan ƙungiyar asiri da kuma masu safarar miyagun ƙwayoyi a jihohi da suka haɗa da Borno, Adamawa, Zamfara, Kaduna, Benuwe, Kwara, Nasarawa, Imo, Anambra, Delta, Bayelsa da Ribas.
- Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Gwamnatin Amurka Ta Tsayar Da Ayyukanta
- PENGASSAN Ta Dakatar Da Yajin Aikin Da Ta Fara
Sojojin sun ƙwato bindigogi, harsasai, bama-bamai, babura, man fetur da aka sarrafa ba bisa ƙa’ida ba da kuma tarin miyagun ƙwayoyi.
A Zamfara da Kaduna, sojoji sun ceto waɗanda aka yi garkuwa da su tare da kama ƙasurguman shugabannin masu garkuwa da mutane, yayin da a Benuwe da Kwara aka kuɓutar da fasinjoji da mazauna ƙauyukan da aka sace a wasu hare-hare daban-daban.
A Kudu maso Kudu kuma, jami’an tsaro sun ƙwato sama da lita 1,200 na man dizal da ɗanyen mai da aka sarrafa ba bisa ƙa’ida ba tare da haɗin gwiwar hukumar NDLEA wajen daƙile hanyoyin safarar miyagun ƙwayoyi.
Majiyoyin tsaro sun ce waɗannan hare-haren wani ɓangare ne na yunƙurin karya ƙarfin ’yan ta’adda da kuma katse hanyoyin samun kuɗaɗensu ta hanyar safarar miyagun ƙwayoyi, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma sata man fetur.
Sun kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da ba da bayanai ga hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen ayyukan ’yan ta’adda da ’yan bindiga a faɗin ƙasar.