Dakarun sojin Operation HADIN KAI sun kashe ‘yan Boko Haram 13 da suka yi yunƙurin kai musu hari da bama-bamai a yankin a Jihar Borno.
Harin ya faru ne a ranar Laraba, 3 ga watan Satumba, 2025, lokacin da sojojin ke rakiyar wasu motoci masu ɗauke da kayan agaji a kan hanyar Gubio zuwa Damasak.
- Gwamna Sule Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Fara Yaƙin Neman Zaɓe A Nasarawa
- Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Ba Da Gudummawarta Wajen Kiyaye Zaman Lafiya Da Ci Gaban Duniya
Mai magana da yawun rundunar, Laftanal Kanal Sani Uba, ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun tada bama-bamai guda biyu sannan suka fara harbin sojojin.
Ya ce sojojin sun yi gaggawar mayar da martani, inda suka kashe ‘yan ta’adda 13 nan take, sauran kuma suka gudu.
Bayan haka, sojojin sun bi sahun ‘yan ta’addan inda suka ƙwato bindigogi AK-47 guda takwas, harsashi da dama, jaka, da igiyoyin da ake amfani da su wajen yin bama-bamai.
Sai dai soja ɗaya ya samu rauni kaɗan amma yana cikin koshin lafiya.
Haka kuma sun lalata tayoyi guda huɗu na mota, sannan manyan motoci biyu sub kama da wuta a yayin arangamar.
Laftanal Kanal Uba ya ƙara da cewa sojojin na ci gaba da gudanar da ayyuka a yankin domin hana ‘yan ta’adda damar kai hari tare da tabbatar da kayan agaji sun isa Damasak lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp