Hedikwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarunta da ke aiki a jihohi daban-daban na cikin gida sun kashe ‘yan ta’adda 92 ciki har da wani Kasurgumin kwamandan ‘yan ta’adda, Abba Alai wanda aka fi sani da Amirul Khalid na Alafa, sannan dakarun sun kama wasu 111, yayin da aka kubutar da mutane 75 da aka yi garkuwa da su a cikin mako guda.
Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Markus Kangye ne ya bayar da wannan adadi a ranar Alhamis yayin bayyana ayyukan sojoji na mako-mako tsakanin 27 ga Fabrairu zuwa 6 ga Maris 2025.
- Yadda Fadada Bude Kofar Kasar Sin Ke Haifar Da Damammaki Ga Duniya
- Xi Jinping Ya Ziyarci Mambobin Majalisar CPPCC
Ya ce, sojojin sun kama mutane 18 da ake zargin barayin man fetur ne tare da kwato man da darajarsa ta kai Naira miliyan 521,802,360.00.
Maj.-Gen. Kangye ya kara da cewa dakarun da ke yaki da satar mai sun kwato lita 452,396 na danyen mai da aka sata, lita 224,175 na Man gas da aka tace ba bisa ka’ida ba, da kuma lita 1,920 na man fetur.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp