Dakarun rundunar ‘Operation FANSAN YAMMA (OPFY)’ sun kashe ‘yan ta’adda da dama tare da kubutar da wasu mutane tara da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.
A wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar OPFY, Kaftin Adewusi David, ya fitar, ya ce an samu nasarar hakan ne a wani harin kwanton bauna da aka kai a karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara da yammacin ranar Lahadi, 31 ga watan Agusta, 2025.
- NAPTIP Da Hisbah Sun Ceto Mata 12 Da Aka Yi Safararsu A Kano Zuwa Saudiyya
- Antonio Guterres: Xi Jinping Shugaban Kasa Ne Mai Sanin Ya Kamata
Ya ce, harin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da suka tabbatar da cewa, anga tafiyar wasu ‘yan ta’adda a wani fitacce wuri tsakanin Isa zuwa Shinkafi zuwa Kaura Namoda, wanda ya hada jihohin Zamfara da Sokoto.
Ya kara da cewa, sojojin sun yi kwanton bauna ne domin farmakar ‘yan ta’addan, amma da suka lura da kasancewar sojojin a yankin, sai suka yi yunkurin boyewa jikin mutanen da suka yi garkuwa da sun.
“Amma sojojin sun fatattake su cikin dabara da kaifin hikima wanda hakan ya haifar da kashe wasu daga cikin ‘yan ta’addan yayin da sauran suka tsere da munanan harbin bindiga” in ji Kaftin David
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp