Dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) a Arewa maso Gabas sun kashe ‘yan ta’addar ISWAP shida a garin Banki da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno.
Jami’an tsaro na musamman tare da hadin gwiwar Civilian Joint Task Force (CJTF) ne suka kashe ‘yan ta’addan a ranar Alhamis, 22 ga watan Yuni, 2023 a wani harin kwanton bauna da suka kai a kusa da titin Bula Yobe da Darajamal, a karamar hukumar Bama.
- Wakilan Sin Sun Yi Kira Da A Inganta Kwarewar Afirka A Fannin Dakile Ta’addanci
- Mutum 2 Sun Shiga Hannu Kan Fashin Katin ATM A Kaduna
Wani kwararre a fannin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun dasa bama-bamai ne, wadanda galibi ke kan hanya don kai harin kwantan bauna kan sojojin.