Rundunar bincike ta haɗin gwuiwa (Joint Investigation Centre – JIC) ta bayyana cewa an kammala bincike kan laifukan da ake zargin ‘yan ta’adda 1,450 da su, kuma suna jiran a gurfanar da su a gaban kotu.
Muƙaddashin kwamandan cibiyar, Kanal AU Ahmed, wanda Kyaftin Olugbenga Adeniyi ya wakilta yayin da yake ganawa da manema labarai, ya bayyana cewa waɗanda ake shirin gurfanarwar suna cikin mutane 1,877 da ake ci gaba da bincikensu a cibiyar.
- Sojoji Sun Harbe Wani Ɗan Bindiga, Sun Ƙwato Makamai Bayan Artabu A Taraba
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Dama A Wani Sabon Hari Da Suka Kai Sansanin Sojoji A Borno
Kanal Ahmed ya ce waɗanda aka kammala bincike akansu amma aka samu ba su da hannu a ayyukan ta’addanci, an tura su domin gyaran hali ko kuma shirin cire musu tsattsauran ra’ayi (deradicalisation), yayin da waɗanda aka tabbatar da laifinsu aka tura su cibiyar giwa a Kainji domin shari’a.
Ya ce bayan kammala bincike, ƙungiyar nazarin manyan laifuka (Complex Casework Group – CCG) na duba rahoton binciken da kuma bayar da shawarar doka. Bisa ga wannan, ana ware waɗanda za a gurfanar da su, da waɗanda za a gyara su, da kuma waɗanda za a maido cikin al’umma.
Ya ce cibiyar na fuskantar ƙalubale wajen samun shaidu da kuma jinkirin gurfanar da ‘yan ta’adda gaban kotu , duk da cewa tana yin duk abin da doka ta shimfida a kanta. Wannan jinkiri, in ji shi, na kawo tsaiko da haifar da matsaloli ga kokarin yaƙi da ta’addanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp