Sojojin Runduna ta 3, ta Operation Safe Haven (OPSH) sun kwato wasu makamai da ƴan bindiga suka tsere suka bari a hanyar Kampani zuwa Kombodoro a ƙaramar hukumar Wase, Jihar Filato.
Makaman da aka samu sun haɗa da bindigar AK-47 guda ɗaya, magazin ɗin AK-47 guda biyu da harsashi 7.62mm (na musamman) guda biyar. Jami’in hulɗa da jama’a na OPSH, Manjo Samson Zhakom, ya bayyana a Jos cewa Sojojin sun yi kwanton ɓauna bayan sun hangi ƴan bindigar da ke kan babura ɗauke da bindigogi, inda suka far musu da luguden wuta har suka tsere.
- Sojoji Sun Ƙi Karɓar Cin Hancin Miliyan 13 Daga Ƴan Ta’adda A Filato
- Sojojin DRC: Ƴan Tawayen M23 Sun Kashe Fararen Hula 17
Sanarwar ta ce makaman da aka kwato na hannun Sojojin yanzu haka, kuma suna ci gaba da bin sahun ƴan bindigar da suka tsere. Haka kuma, a ranar 22 ga Yuli 2025, Sojojin sun ceto wani yaro ɗan shekara 12 a wani sumame da suka kai a maɓoyar masu laifi a yankin Riyom.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa, wani kawun yaron ne ya sayar da shi shekaru uku da suka gabata, wanda yanzu haka ya tsere ba a san inda yake ba. An miƙa yaron ga Kansilan da ke wakiltar Mazabar Zamko a ƙaramar hukumar Langtang ta Arewa domin haɗa shi da iyayensa.
Kakakin ya ƙara da cewa Sojojin na ci gaba da ƙoƙari da samun nasarori a yaƙi da masu miyagun laifuka domin tabbatar da tsaron ƙasa baki ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp