Rundunar hadin gwiwa ta ‘Operation HADIN KAI’, OPHK da ke aiki a Arewa maso Gabas, ta mikawa gwamnatin Borno mutane 75 da ta ceto.
Taron wanda aka gudanar a ranar Litinin, ya samu halartar wakilan gwamnatin Borno, da jami’an soji, da masu ruwa da tsaki na ayyukan jin kai da ke aiki a jihar.
- Hukumar Kwastam Da DSS Za Su Yi Hadin Gwiwa Don Yaki Da Masu Fasa-kwari
- Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Kano, Sun Sace Mutum Ɗaya
Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban jama’a, Zuwaira Gambo ta samu wakilcin daraktar jin dadin jama’a Asher Shettima.
Da yake jawabi a wurin taron, Maj.-Gen. Waidi Shuaibu, kwamandan OPHK, ya ce matakin na daga cikin kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya a yankin da kuma dawo da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.
Shuaibu ya jaddada aniyar rundunar na dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas ta hanyar kawar da barazanar masu tada kayar baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp