Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya (NAF) ta ƙaddamar da hare-haren sama da suka yi nasara kan maɓoyar ƴan ta’adda a jihohin Kaduna da Zamfara, inda ta kashe ƴan ta’adda masu yawan gaske.
An kai harin ne a ranar 21 ga Agusta, 2024, bayan samun wasu bayanan sirri da suka gano dajin Mallum a Jihar Kaduna a matsayin sansanin ‘yan ta’adda da ke da alhakin hare-haren baya-bayan nan a ƙaramar hukumar Shiroro a Jihar Neja.
- ‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Uwan Da Suka Birne Matashi Da Ransa A Kaduna
- Anyi Garkuwa Da Hakimi Da Wasu Mutane Biyar A Kaduna
A cewar mai magana da yawun NAF, AVM Edward Gabkwet, ƴan ta’addan sun koma dajin Mallum bayan sun tsere daga dajin Alawa a Jihar Neja.
An kai hari da jirgin sama kan sansanin ƴan ta’addan, inda majiyoyi daga yankin suka tabbatar da mutuwar ƴan ta’adda da dama.
Haka zalika, a wani harin makamancin wannan da aka kai a ƙaramar hukumar Maradun a Jihar Zamfara, an samu nasarar hallaka ƴan ta’adda a maboyar su da ke Bayan Ruwa, inda aka bibiyi su har zuwa inda suka buya.
Bugu da kari, ɓangaren NAF a ƙarƙashin Operation Delta Safe ya lalata wuraren tace haramtacce mai sama da 25 da kuma tankokin ajiya a yankin Niger Delta. Hare-haren sun shafi yankuna a jihohin Imo da Ribas, inda aka dakile ɓarnar muhalli da kuma gyaran bututun mai da ke yoyo a Greenville, Jihar Ribas, wanda ya miƙa har zuwa nisan mita 150.