Rundunar sojojin Nijeriya ta 6 mai hedikwata a Jalingo, ta bayyana aniyar ta na fatattakar ‘yan bindiga, da masu garkuwa da mutane, tare da dakile duk wasu miyagun ayyuka a Taraba.
Kwamandan rundunar, Maj.-Gen. Frank Etim ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wani taro na hadin gwiwa da rundunar hadin gwiwa da runduna ta 6 da bataliya ta 114 (WASA) 2023 da aka gudanar a Jalingo. Etim ya bayyana cewa rundunar za ta tabbatar da samar da isasshen tsaro ga al’ummar jihar.
- An Sace Mai Ciki, Hakimi Da ‘Yansanda A Taraba
- CBN Ya Ruguza Shugabannin Gudanarwar Bankunan Union, Keystone, Polaris Da Titan Trust
Ya kuma yabawa mutanen jihar bisa hadin kai da goyon baya da suke ba wa rundunar, musamman wajen samar da bayanan sirri kan lokaci na ayyukan ‘yan ta’addan da sauran masu aikata miyagun ayyuka a jihar.
Kwamandan ya kuma mika godiyarsa ga gwamnatin jihar bisa goyon bayan da ta ke ba su wajen magance matsalolin tsaro a jihar.
Ya kuma bukaci jami’an rundunar da su kara himma wajen tunkarar matsalolin tsaro a jihar.