Sojoji sun yi nasarar kashe ‘yan ta’addar kungiyar Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihad da aka fi sani da Boko Haram su kimanin 160 tare da lalata maboyarsu sakamakon wani hari da rundunar sojojin saman Nijeriya suka kai musu ta jiragen yaki a jihohin Borno da Yobe.
Rundunar sojin sama ta Operation HADIN KAI ce ta kai wannan harin kan maboyarsu biyu da aka gano a ranar Alhamis, 2 ga watan Nuwamba, 2023.
- Bam Ya Yi Ajalin Mutane 20, Ya Jikkata 2 A Yobe
- Jiragen NAF Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Lalata Baburansu 40 Da Bindigu 6 A Borno
Maboyar ‘yan ta’addar da harin sojojin saman ya ritsa da su sun hada da maboyarsu ta yankin Bulabulin daura da kogin Komadugu-Yobe kusa da Geidam a jihar Yobe.
Wani mai sharhi kan harkokin tsaro kuma kwararre kan yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana cewa harin da aka kai a yankin Bulabulin daura da kogin Komadugu-Yobe an kai ne kan babbar cibiyar Boko Haram, inda ‘yan ta’addar daga baya suka hada kai suke gudanar da ayyukansu a wurin.