Dakarun rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ta samu nasarar hallaka ‘yan fashin daji 22 a kananan hukumomin Batsari da Jibiya da ke Jihar Katsina.Â
‘Yan ta’addan da ke karkashin kasurgumin mai garkuwa da mutane, Abdulkareem Boss, sun bakunci lahira sakamakon farmakin da dakarun sojin saman Operation Hadarin Daji suka kai musu a ranar Litinin.
- ‘Yan Fashin Daji Sun Tsere Yayin Da Sojoji Suka Yi Wa Dajin Kaduna Kawanya
- An Rufe Makarantu A Kenya Saboda Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa
Wasu majiyoyi sun shaida wa PRNigeria cewa jiragen NAF sun kai jerin hare-haren ne bayan samun rahoton sirri da nuna cewar ‘yan ta’addan suna yi garkuwa da mutanen dama tare da kai hari ga wasu kauyuka da suke cikin karamar hukumar Kankara a jihar.
Daya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa, “Rahoton sirri ya gano cewa wasu ‘yan ta’adda da yawa da suka buya cikin yankunan, sun shirya yadda za su kai wa mutane hari a hanyar Jibiya zuwa Katsina.”
Majiyar ta ce, “Samun bayanin ke da wuya dakarun NAF suka kai samame da nufin tunkarar ‘yan fashin dajin kuma cikin nasara suka kashe da dama tare da tarwatsa inda suke buya.”
Idan za a tuna dai a ranar 6 ga watan Agustan 2022 ne jirgin yakin NAF ya kai hari ga ‘yan fashin dajin tare da kashe shugabansu, Alhaji Abdulkareem Lawal da aka fi sani da Kareem Boss, tare da wasu mutanensa a dajin Ruga da ke Katsina.
Da aka tuntubi kakakin rundunar sojin sama, Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da harin baya-bayan nan da suka kaddamar a ranar Litinin, sai dai bai bada cikakken bayani ba.