Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) a ƙarƙashin atisayen (Operation) HAƊIN KAI (OPHK) ta kai hare-hare kan sansanon ‘yan ta’adda guda biyu a yankin Sambisa da Kudancin Jihar Borno.
Harin saman, wanda aka kai ranar 15 ga Afrilu, 2025, ya biyo bayan sahihan bayanai na sirri game da manyan kwamandojin ‘yan ta’adda da ke yankin, inda aka gano gine-gine da dama, wasu suna da na’urorin hasken rana, wanda aka bayyana su a matsayin manyan sansanonin ‘yan ta’adda.
- Samarwa Matasa Abun Yi Shi Zai Kawo Ƙarshen Ta’addancin Boko Haram Da ‘Yan Bindiga – Zulum
- ‘Yan Ta’adda Sun Tarwasta Gadar Mandafuma A Jihar Borno
A cikin wata sanarwa, Jami’in hulɗa da Jama’a na NAF, Ehimen Ejodame, ya bayyana cewa an kai harin farko kimanin ƙarfe 5:30 na safiya a Kollaram, wani sanannen sansanin ‘yan ta’adda. Ya ƙara da cewa harin ya biyo bayan rahotannin sirri da hotunan binciken jiragen sama da suka tabbatar da kasancewar manyan kwamandan ‘yan ta’adda a yankin. Daga bisani, NAF ta aiwatar da harin don halaka ‘yan ta’addan da yawa da kuma lalata muhimman kayan aiki.
A harin na biyu, wanda aka kai a kimanin karfe 3:55 na yamma a Arra cikin Sambisa, an samu nasarar gano taruwar ‘yan ta’adda da kuma tabbatar da manyan masu shiga cikin wannan yanki.
Ejodame ya bayyana cewa an yi amfani da makaman da aka nufa daidai, wanda ya kai ga hallaka sansanonin da kuma katse ikon aikin ‘yan ta’adda. Ya ƙara da cewa waɗannan hare-haren wani shiri da aka daɗe ana tsara wa don rage ƙarfin ‘yan ta’adda, da kashe jagororinsu, da kuma kawar da wuraren da suke fakewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp