Ma’aikatar tsaron kasar Sin, ta fitar da wata sanarwa a Litinin din nan, wadda ke cewa wakilai daga rundunar sojin ruwan kasar Sin da na kasashen yankin tekun Guinea 19, za su gudanar da taro karo na biyu a birnin Shanghai na kasar Sin, domin tattaunawa game da tsaron teku, taron da ya zai gudana tun daga gobe Talata zuwa ranar Juma’a.
Sanarwar ta ce yayin taron, za a aiwatar da kudurorin da aka amince da su, yayin dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka na FOCAC, wanda ya gudana a birnin Beijing, da ma gina tsarin samar da al’umma mai makomar bai daya ta Sin da kasashen Afirka a sabon zamani, da al’umma mai makomar bai daya ta fuskar tsaron teku tsakanin dukkanin sassan. (Mai fassara: Saminu Alhassan)