Rundunar Sojin Sama (NAF) ta ce hare-haren ta na sama sun kashe ‘yan bindiga da dama, ciki har da manyan mambobin ɓangarorin Dan-Isuhu da Dogo Sule, a Jihar Zamfara.
Hare-haren sun biyo bayan shirin ‘yan bindigar na kai farmaki ga sojoji ko fararen hula a yankin Tsafe, kamar yadda kakakin NAF, Air Cdre Olusola Akinboyewa, ya bayyana a yau Lahadi.
- Mayakan FPL 9 Sun Mika Wuya Ga Gwamnatin Sojin Nijar
- NAF Ta Kashe ‘Yan Ta’adda A Kaduna, Ta Ceto Mutanen Da Suka Sace
Harin ya kasance cikin ci gaba da atisayen FARAUTAR MUJIYA, wanda aka tsara don kawar da barazanar ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma. A ranar 15 ga Nuwamba, 2024, sashin sama na Operation FANSAR YAMMA ya kai farmaki a ƙauyen Babban Kauye da ke ƙaramar hukumar Tsafe, inda aka kashe ‘yan bindiga da dama yayin da suke taro suna shirya kai farmaki. Rahotanni sun tabbatar da cewa an kawar da wasu manyan shugabannin ‘yan bindiga, wanda ya rage ƙarfin ayyukan su sosai.
Babban Kauye ya kasance mafaka ta tsawon lokaci ga ‘yan bindiga, inda suke shirya hare-haren su daga yankunan karkara da suka mamaye. Wannan farmaki na baya-bayan nan yana da nufin karya karfin gwuiwar su tare da hana kai hare-haren da suke shirin yi, domin dawo da zaman lafiya a yankin.
Kakakin NAF ya tabbatar da cewa za su ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da kwanciyar hankali a yankin Arewa maso Yamma da kuma ƙasa baki ɗaya.