Dakarun rundunar Sojin saman Nijeriya (NAF) sun lalata wasu mahimman wurareda suka kasance maboyar ‘yan ta’adda tare da daƙile wani harin da aka shirya kai wa yayin bukukuwan Sallah a jihar Borno.
Wata sanarwa daga mai magana da yawun NAF, Air Commodore Ehime, ta bayyana cewa hare-haren jiragen sama sun gudana tsakanin ranar 5 zuwa 6 ga watan Yuni, 2025.
A cewar sanarwar, an gudanar da wannan farmaki ne a ƙarƙashin Operation HADIN KAI, inda jiragen yakin suka kai hari kan sansanonin Boko Haram da ke Tumbumma Baba da Chira5lia a Kudancin yankin Tumbuns.
- Sojoji Sun Daƙile Harin Ƴan gg, Sun Kashe Wasu Da Yawa A Borno
- DSS Da Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 45 A Neja
An kai harin ne bisa sahihin bayanan sirri da suka nuna cewa gine-ginen da aka kai wa hari na ɗauke da kayan aiki da ake amfani da su wajen shirya hare-hare. Harin ya hana aiwatar da shirin barnar da ‘yan ta’addan suka yi niyya a lokacin bikin Sallah.
Ejodame ya ƙara da cewa wannan matakin gabanin lokaci ya nuna irin jajircewar NAF wajen kare rayukan fararen hula da tabbatar da tsaron kasa.