Somaliya ta bi sahun wasu kasashe wajen haramta TikTok, da kuma hanyar aika sakon Telegram da Intanet na 1DBet domin dakile yada ayyukan batsa da lalata da wasu abubuwan da ba su dace ba da kuma farfaganda, in ji ministan sadarwar kasar.
“Ministan sadarwa ya umarci kamfanonin intanet da su dakatar da aikace-aikacen da aka ambata a baya, wadanda ‘yan ta’adda da kungiyoyin fasikanci ke amfani da su wajen yada munanan hotuna da kuma labaran karya ga jama’a,” in ji Ministan, Jama Hassan Khalif a wata sanarwa da ya fitar.
Mambobin kungiyar masu ta da kayar baya ta Al-Shabaab su kan yada ayyukansu ne akan TikTok da Telegram.
Matakin na zuwa ne kwanaki bayan shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud, ya ce, farmakin soji kan kungiyar Al-Shabaab na da nufin kawar da kungiyar da ke da alaka da Al-Kaeda nan da watanni biyar masu zuwa.
TikTok, Telegram da 1DBet nan take ba su ce uffan ba, a lokacin da Reuters ya nemi su yi tsokaci kan lamarin.
Umurnin ya ba masu ba da sabis na intanet su fara aiwatar da wannan tsari nan da zuwa ranar 24 ga watan Agusta.
An yi barazanar haramta TikTok da saka masa takunkumi a Amurka saboda alakarta da Gwamnatin China.
Jihar Montana ta zama ta farko da ta haramta amfani da manhajar a watan Mayu.