Kocin Ingila Gareth Southgate ya yi murabus bayan rashin nasara a gasar cin kofin nahiyar Turai karo na biyu a jere.
Tawagar ta Three Lions ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Spain a birnin Berlin ranar Lahadi.
- Dan Majalisar Tarayya Ekene Daga Kaduna Ya Rasu
- Trump Ya Zabi Mai Shekaru 39 A Matsayin Mataimakinsa
Kazalika kasar Italiya ta doke su a bugun fanariti a Wembley shekaru uku da suka wuce.
Kocin mai shekaru 53 ya jagoranci kasarsa wasanni 102 a cikin shekaru takwas.
Kwantiraginsa zai kare ne nan gaba a wannan shekarar.
Southgate ya ce “A matsayina na dan Ingila, ya zama abin alfahari ga rayuwata na buga wa Ingila wasa na kuma horar da babbar tawagar kwallon kafar kasar, hakan babban abin alfahari ne gare ni kuma na bayar da duk wani abu da ya kamata.
“Amma lokaci ya yi da za a nemi canji domin samar da sabon babi a tarihin wannan tawagar kwallon kafa ta kasar Ingila mai dimbin jajirtattun yan wasa da masu horarwa”.
Southgate shi ne koci na farko tun bayan Sir Alf Ramsey wanda ya lashe kofin Duniya a shekarar 1966 da ya jagoranci tawagar kasar zuwa wasan karshe na kowace irin gasa.
Ya jagoranci Ingila a manyan gasa hudu, sannan ya kai wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya a shekarar 2018 da kuma wasan kusa da na karshe a shekarar 2022.
Southgate ya kara da cewa tawagar da muka tafi dasu Jamus na cike da matasa masu hazaka kuma za su iya lashe kofunan da muke fatan lashewa anan gaba.
Daga karshe yace “Nagode Ingila ina muku fatan alheri”