Shafin daya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya da dai sauransu. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda kananan yara wadanda ba su haura shekaru 13 zuwa 14 ba, ke fadawa tafkin soyayya, koda kuwa iyayensu na kokarin basu ilimin rayuwar da ta dace, sukan yi kokarin kara iza wutar soyayyar samari dake cikin zuciyarsu ko da kuwa a boye ne.
Wannan ya sa shafin TASKIRA ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; Ko mene ne ribar fara soyayya ga ‘ya mace me kananun shekaru?, Wanne bambanci soyayyar mace me kananun shekaru da kuma wadda take daidai minzalin aure yake da shi?, Me yake janyo hakan game da kananan yara? Wadanne irin matsaloli hakan ka iya haifarwa? Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka;
- Kotu Ta Dakatar Da Biyan Miliyan 10 Kuɗin Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukuma A Kano
- Fim Din ‘Princess Of Galma’ Zai Zo Da Wani Bakon Tsari A Kannywood -Jammaje
Sunana Rahinat Mahmud Nijar/Niamey:
A tunanina da kuma nazarin da na yi, gaskiya hakan bai da wani riba, domin kuwa za ta bata rawarta da tsalle. Ni dai a ganina babu wani bambanci, domin yaran yanzu babu irin kallar soyayyar da ba su iya ba. Zumudi da hudubar kawaye, da kuma rashin sauraran maganar magabata. Da na sani marar amfani, domin yara da yawa za su rasa darajarsu da mutuncinsu, dama Hausa sun ce idan ba ka ji bari ba – ka ji oho. Shawarata shi ne, su cigaba da yi wa yaransu addu’a, addu’ar iyayye ba za ta taba faduwa a kasa ba. Allah Ubangiji ya shiryamu baki daya Allahumma Amin.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya batun fara soyayya da karancin shekaru wani abu ne da ka’iya cewa yana faruwa ne ba zato ba kuma tsammani, domin ita soyayya wata aba ce da Allah yake dasa ta a tsakanin mutane biyu, don haka ribar ita ce ayi ta bisa tafarkin da addinin musulunci ya tsara kuma hakan kar ya zama silar watsar da neman ilimi domin ilimi shi ne gishirin zaman duniya. To ita soyayya tsakanin yarinya mai karamin shekaru da kuma matashi babu wani bambanci ta fuskar so amma banbamci shi ne ta fuskar yadda za su ke mu’amula da kai ta wajen lafazi da kuma sanin ya kamata dole banbamcin shekaru zai nuna a tsakaninsu. Magana ta gaskiya a yanzu tasirin zamani a cikin dabi’un al’umma shi ne yake jawo haka, kuma mafita a cikin wannan al’amari shi ne duk lokacin da hakan ta faru to iyaye su yi hakuri su bari ayi auren domin shi ne kadai mafita a cikin wannan al’amari, kokarin hana yin auren yana iya haifar da matsaloli da dama. To magana ta gaskiya a wasu lokutan za ka ga idan an yi soyayyar kuma aka yi auren a irin wannan shekaru to ana samun matsaloli na rashin sanin cikakken manufar auren kuma ake samun matsalar rashin ganin darajar juna da dai sauran su. To da farko dai addu’a ce mafita da fatan Allah ya shirya maka yara ya baka ikon tarbiyyar su akan tafarki madaidaici, na biyu kuma ka kula da abokan mu’amular su tun daga makaranta har gida da kuma Jan su a jiki domin ba su shawara da kuma sanin matsalar su domin magance ta a lokacin daya dace. Daga karshe nake addu’ar Allah ya shirye mu gaba daya akan tafarki madaidaici.
Sunana Aisha Isah Abubakar (Aisha Gama Mai Waka), Jihar Kano:
A gaskiya ba shi da fa’ida yarinya ta fara soyayya tana da kananun shekaru kai tsaye. Abu na gaba da babbar budurwa wacce iyayenta sun shirya aurar da ita ba hadi sabida an shirya, wata kila ta gama karatu. Cudanya da kawaye wadanda suke da ra’ayin soyayya tun kafin su tafasa balle su kone, Allah ya shirya mana zuriya ba dan halinmu ba sabida Annabi (S.A.W). Ai indai aka bari hakan ta faru komai ya tabarbare sai dai addu’a, sabida komai zai iya faruwa, Allah ya shirya mana zuriya. A gaskiya indai har Allah ya azurta mu da ‘ya mace wallahi aiki ya same mu dan sai mun tsaya mun dage mun rike amanar da Allah ya ba mu domin zai tambaye mu, Allah ya taya mu riko ya kare mana zuriya ya shirya mana su baki daya. Ina Jan hankalinmu ‘ya macannan fa ita ce lasisinmu na shiga aljannah, sannan ita ce lasisinmu na shiga wuta, Allahumma Ajirni Minan Naar, domin ayki ne ya same mu ja musamman iyayen mata Allah ya tayamu ruko Allah kuma ya sa mu gama da duniya lafiya Ameen ya hayyu ya kayyum.
Sunana Nasiru Kainuwa Hadejia:
Ba shi da wani amfani yarinyar da ba ta wuce shekaru 14 ba ta kasance ta na soyayya. Ko iyaye da kakanninmu da aka yi musu auren wuri ai basu yi soyayya irin wacce yaran yanzu ke yi ba. Wasu an aurar da su ne ma ba tare da sun taba yin soyayyar ba. Soyayya dai daya ce, irin wacce ‘yan mata ke yi, ita ce wacce kwailaye ke yi, kalubale ne ga iyaye na su kula da ‘ya’yansu. Kallace-kallacen fina-finai na soyayya, da karance-karance ko sauraren labarai na soyayya su na da kaso hamsin dake jefa yara mata fagen soyayya kafin iyayensu su farga. Sannan akwai talla ko kuma yawan mu’amala da maza koda yarinya ba ta talla. Duk yarinyar da ta fara soyayya da kananan shekaru abu ne mai sauki ta lalace, ko ta zama mai tsaurin ido ko ta fara shafe-shafe (bleaching) da makamantan haka. Irin su ne kuma wanda in iyayensu suka kawo musu wanda zai aure su suke bujirewa. Mafita iyaye ku sa ido ga ‘ya’yanku kamar yadda shari’a ta ce, ku rika yi musu adu’a, kada ku yi tsananin da kuma zai zama takura gare su, domin hakan nasa wasu lalacewa. Uwa ki kula da ‘yar ki, ke ki ka haife ta duk yadda za a yi ki tabbatar kin zama tamkar kawarta yadda ba za ta boye miki sirrinta ko wata damuwarta ba. Kai kuma uba ci da sha, tufatarwa da sauran dawainiya hakki ne a kanka. Ka dauki dauniyar ‘yarka ko kuma wani a waje ya dauka.
Sunana Sadiya Garba, Jihar Kano:
Abin da zance anan shi ne idan har ku ka fahimci inda hankalin yaranku ya fi karkara to Alal hakika ku barsu su yi idan soyayyar ce a ransu tofa ba za su taba yin abin da ku ke so ba ‘especially at this time around 13-14y’ suna jin kansu daidai da kowa ne. Bai kamata mu bar ‘under age’ su fara soyayya ba amma ina ga 14y ai sun zama ‘adolescent’ kuma gama ‘secondary sch’ yana farawa ne daga 16-17y idan har auren za:kaiwa yaro a wannan lokacin za ka iya masa ba matsala bane. Eh! akwai bambancin shi ne me kananan shekaru tanada rangwamen hankali bata san me yake mata ciwo ba kawai abin da take so shi take kallo bata tunanin me zai je ya dawo wadda take da shekaru sosai duniya tana koya mata hankali tana sani meye zai zamar mata alfahari a gaba. Samari ne suke dauke musu hankali da kalaman soyayya da kuma kawata su akan halittar su. Eh to ana iya samun matsala idan iyaye suka takurawa yaransu kan sai sun yi karatu su kuma yaran aka yi rashin sa’a akan hankalinsu baya kan karatun sai ka ga ‘at the end’ yarinya tana tafiya dakin saurayin ku kuna ganin makarantar ta tafi. Ni dai shawara shi ne idan har yarinya ta nuna bata son karatu kar ayi mata dole ayi mata abin da take so kawai, sannan su saka ido akansu saboda sai kayi shekara da shekaru kana baiwa yarinyar ka horo na tarbiyya rana daya wani ya zo ya tarwatsa maka wannan tanadin.
Sunana Isyaku Director, Karamar Hukumar Shiroro Jihar Neja:
Rayuwa mai kyau sai dai mai kyau ake samun kyau, dan haka babu riba ga ‘ya mace mai kananun shakaru a soyayya saboda, ita karan kanta soyayya wata kwayar halitta ce wacce Allah subhanahu wata’alah ya sakata tayi rayuwa a cikin zuciyoyin halitto musanman dan Adam wanda Allah ya fiffita halittarsa alfarman manzon Allah (s.a.w). Dan haka yin soyayya ga yara masu kananun shakaru illah ce babba wacce ta ke kawo lalacewar tarbiyyar ‘ya’ya mata, Ya kan hanasu karatu Idan har suna makaranta. Soyayyar wuri ga ‘ya’ya mata ya kansa wasu iyayen rasa alkibilar yayansu a rayuwa, ya kan haifar da kunci, ciwon zuciya, da kuma rasa rayuwar ma gabadaya, saboda rashin karacin ilimi da hankali da kuma rashin sanin yadda za su dauki soyayyar domin karancin ilimi da kuruciya wacce hausawa ke yi wa lakabi da kuruci dangin hauka. Tabbas! akwai bambancin soyayya tsakanin karamar yarinya da babba wacce ta isa aure, Bambancin shi ne; wacce ta’isa aure ta san kima da martaba na masoyanta, wacce ake kira kyautatawar masoya, wanda a soyayyar mace mai karancin shakaru babu hakan saboda karancin wayewa, da kuma kuruciya maisa shirme, Rashin hankali, Rashin iya magana, Rashin sanin tsari kima da kuma martaban ‘yan’uwanka, saboda hankalinta bai kai mizanin fuskantar alkibilar soyayyar ba. Abin da kesa kananun yara masu kananun shekaru fara soyayyar wuri shi ne; Rashin iyaye na gari, Rashin Hankali, Maraici. Matsalolin da ake samu game da soyayyar wuri shi ne; Rashin biyayya ga iyaye, Rashin fahimtar alkibilar duk wani mai bata shawara saboda soyayya ta riga ta rufe mata ido. Shawarar daya kamata iyaye su yi amfani da ita; Saka ido ga yayansu mata sosai, a kula sosai da makarantar su, a kula da irin kawayensu, duk abin da yarinyar take so kuma abin zai amfani inda hali a sai mata.
Sunana Na’ima Sulaiman, Jihar Bauchi:
Babu riba ga fara soyayyar yarinya karama, domin za ta jefa kanta ne a cikin komar da ba za ta iya fidda kanta ba, samari za su samu damar da za su lalata rayuwarta cikin sauki sabida hankalinta bai kai na wadda ta kai lokacin aure ba, duba da yadda shekaru ke karuwa hankali ke zuwa, me karamin shekaru ba ta kai wannan munzalin hankalin ba, ba ta san daidai ba, ba ta san ba daidai ba, sabanin wadda take da hankali za ta iya tantance baragurbi duk da cewa a zamanin nan wadanda ake ganin su ne masu hankalin amma maza na iya yin galaba a kansu har su yaudare su, su bata musu rayuwa bare kuma me karancin shekaru Duk da cewa akwai masu karancin shekarun da hankalinsu ya girmi shekarunsu, tunaninsu ya haura na me shekaru Talata duk da haka tsaya a yi karatu shi ne ya fi dacewa da kananan yara, domin in sun girma ba za su iya ba. Shawara iyaye su kula da ‘ya’yansu soaai musamman mata tare da saka ido yadda ya kamata.
Sunana Abdurrahman Tijjani daga Abuja Nijeriya:
Babu riba, saboda duk soyayyar da ba za ta kai ga aure ba to bata lokaci ne. Soyayyar karamar yarinyar zai shagalar da ita wajan yin abubuwa masu amfani, wadanda za su amfani rayuwarta.. Hakan na faruwa ne sau da dama saboda abun da bature ke kira “peer group” abokanai da suke janyo ra’ayinsu ba tare da sanin iyayensu ba. Lalacewar tarbiyyar yara, saboda sukan yi soyyayar ne da mazan da suka dara su a shekaru. Ya kamata iyaye su yi kyakkyawan buncike wajan sanin irin abokan da yaransu suke da su.
Suna na Bilkisu Maharazu Daga jahar Katsina
Agaskiya Yara Masu kananan shekaru na bukatar ilimi daidai gwargwado saboda rayuwarsu ta yau da kullum, musamman a wannan zamanin da muke ciki,
1) Menene ribar: Babu wata ribar fara soyayya da ‘ya mace Mai kananun shekaru duba da irin halin da ake ciki na rayuwa. Bugu da Kari yadda zata zauna da Mijin shi kanshi, sai tana da ilimi na addini dana boko gaba daya, idan babu daya daga cikin wadannan biyun, za’a iya samun matsala.
2)Akwai banbanci sosai ga mace Mai kananan shekaru da Kuma matashiya wadda take daidai lokacin aure, banbancinsu shine ita matashiya tana da ilimi da tinani wanda yasha banban damai kananan shekaru, tinaninsu bazai zo daya ba.
3)Abunda yake janyo haka da masu kananan shekaru shine yarinta da take damunsu wanda sai daga baya suke hankalta.
4)Yana Iya haifar da matsaloli kamar rashin fahimta ko ilimi wanda baya wuce nasaba da yarinta. Shi kanshi namijin idan ba’a samu mai hankali ba sai su dunga samun matsala. Idan Kuma mai hankali da tinani ne zai ga ai akwai yarinta. Wani Kuma a wurinshi ba haka bane, sai ayi ta samun matsaloli daban daban.
5) Shawara da zan ba iyaye ita ce su dage suga yaransu sun Samu ilimin nan guda biyu musamman ma addini dana boko wadanda su zasu taimaka ma yarinya wajen gudanar da rayuwarta ta yau da kullum musamman a wannan zamanin da muke ciki. Yadda abubuwa suka zama ba kamar nada ba, abubuwa sun chanza sosai.