Kasar Sifen ta Kai wasan karshe na gasar kofin Turai bayan ta lallasa kasar Italiya 2-1 a wasan kusa da na karshe da suka buga a ranar Alhamis.Â
Sifen ce ta Fara jefa kwallo ta hannun Dan wasa Pino a minti na uku da fara wasan amma Ciro Immobile dake buga wasa a Ssc Lazio ne ya farke wa kasarsa ta Italiya kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron raga a minti na 11.
A mintunan karshe na wasanne Joselu ya jefa kwallo a ragar Italiya wanda hakan yasa Sifen ta samu damar buga wasan karshe na gasar kofin kasashen Turai inda zata hadu da kasar Kurotiya wadda ta fitar da kasar Holland a wasan kusa da na karshe da suka buga a ranar laraba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp