Kasar Spain ta kori masu masaukin baki daga gasar kofin kasashen Turai da ake bugawa a kasar Jamus,wasan wanda suka buga a filin wasa na Mercedez Benz ya tashi da ci 1-1 wanda hakan ya sa aka kara mintuna 30.
A minti na 51 da fara wasan Dani Olmo ya jefa kwallo a ragar Jamus kafin Florian Wiltz ya farke a minti na 89 bayan ya amshi kwallo daga hannun Joshua Kimmich kafin ya cilla wa mai tsaron ragar Spain Unai Simon.
- An Wallafa Makalar Da Shugaba Xi Ya Rubuta A Tajikstan
- Ma’aikatan Ruwa Na Jihar Kaduna Sun Yi Zanga-zangar Rashin Albashi
Bayan karin mintuna 30 da alkalin wasa Anthony Taylor ya yi,wasan ya kara zafafa a wajen dukkanin kasashen biyu.
Mikel Merino ya raba gardama a wasan na yau bayan ya jefa kwallo ta biyu ga kasar Spain a minti na 119.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp