- Yadda Kungiyar Ta Mamaye Yankunan Sakkwato Da Kebbi
- An Nemi Gwamnati Ta Gagguta Murkushe Su
Mambobin sabuwar kungiyar ‘yan ta’addar nan mai suna Lakurawa sun kai hari garin Mera da ke Karamar Hukumar Augie a Jihar Kebbi, inda suka kashe mutum 15.
Wani mazaunin garin, Bashir Isah Mera (Yariman Mera) wanda ya tabbatar wa manema labarai harin a garin Argungu, ya ce ‘yan ta’addan sun kai harin ne a daidai lokacin da jama’a ke shirin Sallah tare da kwace shanu akalla 100.
- Sin Ta Kafa Tsarin Ilimin Koyar Da Sana’o’i Mafi Girma A Duniya
- Nijeriya Na Buƙatar Maki 3 Yau Domin Samun Gurbi A Gasar Ƙasashen Afrika
Bayan samun wannan labarin harin ne mazauna garin suka yi ganganku tare da binsu har cikin daji da nufin ceto shanun. Sakamakon musayar wuta da aka yi ya kai ga kashe mazauna garin 15 yayin da aka kashe ‘yan ta’adda biyu.
Isah ya kara da cewa ‘yan ta’addan sun buya ne a wani wuri a Jihar Sakkwato, inda daga nan ne suka hada kai domin hare-harensu, ya ce da farko ba su kashe lowa ba, sai dai kawai sun yi awon gaba da shanu, sannan suka nemi masu su biya haraji.
Hakan dai yana faruwa kusan watanni biyu kuma wannan shi ne harin nasu na farko da ya hada da kisa a Mera, a cewar Isah.
“Gwamnan jihar ya nuna damuwarsa saboda ya yi min waya sau biyu lokacin da ya ji labarin harin, ya kuma aika da sojoji da manyan bindigogi da tankokin yaki domin dakile harin da aka kai garin,” in ji shi.
Ya kara da cewa kwamandan Barikin Sojojin Dukku da daraktan Hukumar DSS da kwamishinan ‘yansanda tare da hadin gwiwar jami’an tsaro sun yi tattaki zuwa yankin tare da ganin komai ya dawo yadda yake.
Sabuwar kungiyar ‘Yan ta’addan sun watsu a kananan hukumomi 5 a na Sokoto
Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar da Sarkin Argungu, Alhaji Samaila Mera, sun kuma ziyarci garin Mera tare da jajantawa iyalan wadanda suka rasu, tare da ba jama’ar jihar da kuma Garin Mera tabbacin kare lafiyarsu.
“Gwamnan ya damu matuka game da harin kuma ya yi alkawarin tabbatar da kariyarsu daga hare-haren kungiyar masu dauke da makamai,” in ji shi.
Mataimakin gwamnan da sarkin ya jagoranci sallar jana’izar marigayin da aka yi jana’izar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a makabartar Augie a jiya.
Ana zargin sabuwar kungiyar na da alaka da Kungiyar ISIS da ke aiki a yankin Sahel.
Rundunar sojin ta tabbatar da kasancewar sabuwar kungiyar a jihohin Sokoto da Kebbi, wanda ta ce bullar tasu ta kara jawo tabarbarewar harkokin tsaro a yankin.
Daraktan Ayyukan Yada Labarai na Tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja, inda ya ce jami’an tsaro na hadin gwiwa sun tabbatar da binciken ‘yan ta’addan.
Buba ya ce sun fito ne daga Jamhuriyar Nijar ne bayan juyin mulkin da ya kai ga rugujewar hadin gwiwar sojoji tsakanin Nijeriya da Nijar.
Ya ce, ‘yan ta’addan sun fara kutsawa cikin Arewacin Jihohin Sakkwato da Kebbi daga Jamhuriyar Nijar da Mali, musamman bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar.
Su Waye Lakurawa?
Jamilu Gulma wakilin jaridar Blueprint ne a Jihar Kebbi wanda ya bibiyi labarin, ya shaida wa BBC cewa, wadansu makiyaya da suke kiwo a garin Mera, ana sa ran ‘yan Lukurawa ne suka kwace dabbobin.
“Sai wani makiyayi ya ruga ya shaidawa mutanen gari abin da ke faruwa, saboda haka matasan garin suka gangami suka zo aka yi ta artabu da su a cikin jejin, inda aka kashe mutum 15 tare da jikkata wasu da dama,” in ji shi.
Jamilu Gulma ya ce mutanen garin sun yi nasarar kashe wasu daga cikin ‘yan bindigar, tare da jikkata wasu da dama, sai dai sun dauke mutanen nasu.
Ko a makon da ya gabata hukumomi da jama’a a Jihar Sokoto da ke makwabtaka da Jihar Kebbi, sun nuna damuwa kan bullar kungiyar Lakurawan masu ikirarin jihadi da ke gudanar da harkokinsu a wasu kananan hukumomin jihar biyar.
Daga ina suke, kuma Mece ce akidarsu
Mataimakin gwamnan Jihar ya shaida wa BBC cewa ‘yan kungiyar wadanda suke dauke da manyan makamai, suna yawo tare da wa’azi ga mazauna yankunan kananan hukumomin Tangaza da Gudu da Illela da Binji da kuma Silame.
Wata majiya ta shaida wa BBC cewa ‘yan kungiyar sun shiga yankunan na Sokoto da Jihar Kebbi ne daga bangaren yankin Sahel da ya kunshi kasashen Nijar, da Mali, kuma mutane ne da suka kunshi kabilu daban-daban na Sahel.
Sukan yi wa’azi tare da shaida wa jama’a irin akidarsu cewa, su ba sa tare da ‘yansanda da sojoji, da ma duk wani jami’in gwamnati na siyasa, kuma ba su yarda da karatun Boko ba.
Masana harkokin tsaro na ganin cewa bullar wannan kungiya ba karamar barazana ba ce ga kasar idan aka yi lakari da cewa wuri ne da fitacciyar kungiya mai ikirarin jihadi a duniya take – Ansaru – kamar yadda Kabiru Adamu na kamfanin Beacon Consulting, mai bincike a kan harkokin tsaro a yankin Sahel ya shaida wa BBC.
Me dattawan Arewa ke fada game da wadannan lamari?
Dattawan Arewa sun yi kira ga sojojin Nijeriya da su kakkabe sabuwar kungiyar ta’addanci a Kebbi da Sokoto.
Dattawan a karkashin inuwar kungiyar koli ta zamantakewar al’ummar Arewa, Arewa Consultatibe Forum (ACF), sun ruwaito cewa ‘yan sabuwar kungiyar ta’addanci mai suna Lakurawa, yanzu haka suna korar mutane daga gidajensu tare da korar jami’an tsaro da ’yan banga a yankunan Nijeriya.
Dattawan sun nuna matukar damuwarsu game da bullar wata sabuwar kungiyar ta’addanci a jihohin Kebbi da Sokoto da ke Arewa maso Yamma, kamar yadda hukumomin yankin da kuma shalkwatar tsaron Nijeriya suka tabbatar.
A cewar sakataren yada labaran kungiyar na kasa, Farfesa Tukur Muhammad-Baba, an ruwaito cewa sabuwar kungiyar tana addabar al’umma tare da korar jami’an tsaron kasar da ‘yan banga na cikin gida, tare da tilasta bin tsarinta na adalci.
“Bugu da kari, ko da yake an ba da rahoton mambobin kungiyar sun zo ne daga kasashen waje (masu magana da Faransanci da yare na harsunan Larabci), an ce suna daukar mambobi ne ta hanyar amfani da karfi.”
ACF ta bayyana bullowar wannan kungiya a matsayin mai matukar hadari da ban tsoro domin hakan na nuni da yadda lamarin tsaro ke kara tabarbarewa a yankin Arewa maso Yamma, wanda yanzu shi ne cibiyar ta’addanci a Nijeriya.
Ya kara da cewa, a yayin da sojojin Nijeriya suka kara kwarin gwiwar fatattakar ‘yan fashi da makami a wannan yanki, wannan lamari ya haifar da damuwa a matsayin wani babban kalubale ga muradun tsaron kasa.
“Don haka bai kamata a yi wasa da kungiyar ta kowace hanya ba kuma dole ne a fatattake su kuma a kula da su ta kowace hanya. Bullowar Lakurawa, a wannan mataki bai kamata a kyale ba, ko a bar su su shiga cikin al’ummarmu ta hanyar rashin kulawa kamar yadda ya faru a rikicin Boko Haram, rikicin manoma da makiyaya da ‘yan fashi a Arewa maso Gabas da yankunan Arewa ta tsakiya, da Arewa maso yamma, bi da bi”.
ACF ta bukaci jami’an tsaro da su gaggauta shawo kan gungun ‘yan ta’addan Lakurawa tare da kawo karshen su ba tare da bata lokaci ba.
“A karo na goma sha uku, ACF ta bukaci da a gaggauta sake duba dabarun tsaro da dabarun tsaron kasa na Najeriya kamar yadda ba kowa zai yi shakkar kudurin kasa na tinkarar duk wata barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya kamar yadda ya kamata. kungiyoyin ta’addanci sun yi la’akari da kowane nau’i ko kwatance.
“Ya kamata a yi amfani da ziyarar da babban hafsan hafsan sojin Najeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya kai Jamhuriyar Nijar a farkon shekarar a matsayin wata nasara don sake sabunta kokarin kasashen duniya na yaki da ‘yan ta’adda.”
Dattawan Arewa sun kuma bukaci gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi da su ba da himma wajen hadin gwiwa mai cike da tarihi da al’adu, tattalin arziki da siyasa da makwabtan Nijeriya wajen fuskantar barazanar tsaro da kungiyoyin ‘yan ta’adda ke yi wa kowa.
ACF ta kuma yi kira da a kara kaimi wajen tattara bayanan sirri tare da yuwuwar shigar masu ba da labari na cikin gida a cikin al’ummomi wajen dakile masu tayar da kayar baya. Dole ne a sanar da mazauna kauyuka ba tare da wata shakka ba, su san illar duk wata alaka da kungiyoyin ta’addanci ta kowace hanya.
Har ila yau, sun bayar da shawarar hadin gwiwa mai inganci a tsakanin hukumomin tsaro na kasa a karkashin hadin gwiwar ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro, da kuma hada kan shugabannin gargajiya da na addini, masu fada a ji, mafarauta, ’yan banga da sauran al’umma don su samu damar gudanar da ayyukansu, samar da jami’an tsaro na tallafawa ayyukan tsaro.
Yadda Jihar Sakkwato ta Shirya Fuskantyar Lamarin ‘yan Ta’addan Lakurawa
Bayyanar sabuwar kungiyar ta’addanci ta Lakurawa da ke hanawa al’umma bacci da idanu biyu ya dauki hankalin gwamnati, hukumomin tsaro da daukacin al’umma musamman kan yadda kungiyar take da dubban mayaka da manyan makaman da suke yi wa al’umma kisan kare dangi.
Fargaba da zaman zullumi sun karu a zukatan al’umma musamman kan yadda salo, dabarun yaki da hadarin kungiyar ya zarce na barayin dajin da suka jima suna cin karensu ba babbaka a Arewa- Maso- Yamma.
Harin da suka kai wa sojoji a Tangaza da ke Sakkwato tare da kashe soja hudu a kwanakin baya da kisan gillar da suka yi wa mutane 15 a kwanan nan a Mera da ke karamar hukumar Augie a jihar Kebbi tare da jikkata wasu ya nuna yadda kungiyar ta fara yakar jama’a gaba da gaba ba kakkautawa.
Tuni masu rike da madafun iko, kungiyar dattawan Arewa, kungiyoyin farar hula da masu sharhi kan tsaro da al’amurran yau da kullum suka yi kira na musamman ga gwamnatin tarayya da ta dauki kwakwaran mataki ta hanyar yin duk mai yiyuwa domin kawar da kungiyar tun kafin ta yi wa Arewa- Maso- Yamma da al’ummarta mummunar illar da za a yi shekaru a na jajantawa.
Kungiyar wadda ke a kananan hukumomin Tangaza, Gudu, Illela, Binji da Silame da ke a jihar Sakkwato babbar barazana kuma kalubale ce ga rayukan alumma da dukiyoyin su wanda idan ba a dauki kwakwaran mataki ba, ba a san irin illar da za ta yi wa al’umma ba.
A ziyarar aikinsa ta farko da ya kai a Sakkwato a Tangaza da Illela, mukaddashin shugaban hafsan hafsoshi, Laftanar – Janar Olufemi Oluyedi ya bukaci jami’an soji da su kakkabe ayyukan ta’addaincin makiya al’umma da ci-gaban kasa ta hanyar farautar ‘yan ta’addan da yaren da suke ganewa, ya kuma bukaci al’umma su baiwa sojoji hadin kai domin samun nasara.
A bayyane Lakurawa suna kai farmaki ga jama’a fiye da ‘yan ta’addan da aka sani, suna kashe jama’a, tilastawa makiya da manoma biyan haraji, yi wa jami’an tsaro kisan gilla da tilastawa jama’a bin tsauraran dokokinsu na addini.
Masana harkokin tsaro sun bayyana cewar kungiyar wadda sunanta ya samo asali daga harshen Faransanci ta bulla ne a Sakkwato tun shekaru shida da suka gabata a 2018 ba wai a yanzu da ake yayatawa ba kamar yadda Bulama Burkati da ke bincike kan harkokin tsaro ya bayyana.
Rahotanni sun nuna cewar sabuwar kungiyar da ke zaune a cikin daji kan baiwa jama’a kariya a yayin da ‘yan ta’adda suka kawo masu hari wanda a kan hakan suka samu karbuwa a wajen jama’a wadanda sai daga baya suka gano illa da hadarin da ke tattare da su.
Masana sun bayyana cewar asalin kungiyar Lakurawa ‘yan kungiyar Al-ka’ida ne da ke karkashin kungiyar JNIM wadanda suka yi suna wajen hana zaman lafiya ta hanyar aiwatar da ayyukan ta’addanci a kaashen Sahel kamar Nijar, Mali Burkina Faso.
Sai dai a Nijeriya kungiyar na tare da kungiyar Ansaru wadda ita ma take a karkashin kungiyar Al’ka’ida kamar yadda mai fashin bakin lamurran yau da kullum kuma dan jarida Aliyu Dahiru Aliyu ya bayyana.
Kungiyar wadda ke magana da harsuna daban- daban suna kuma da Hausawa da ke bayyanawa al’umma sakon su, haka ma su kan fassara sakon su a cikin harsunan Fulatanci, Abzinanci, Barbanci da Turanci domin sakon su ya kai ko’ina.
Salo da dabarun kungiyar ya bambamta kwarai da na barayin daji da aka saba da su domin kuwa sun bayyana ne a cikin salon rigar addinin musulunci a inda suke yin wa’azi ta hanyar fadawa jama’a abin da Allah manzonsa suka ce.
Haka ma hatsabibiyar kungiyar ta nesanta kan ta da karatun Boko tare da kauracewa duk wani lamari da ya shafi gwamnati da musamman jami’an soji da ‘yan sanda tamkar dai kungiyar Boko Haram.
Mazauna yankin Tangaza sun bayyana cewar kungiyar na da mabiya masu yawan gaske suna kuma tallafawa matasa da jari domin su yi sana’a, lamarin da ya ja hankalin matasa da dama ga kungiyar wanda illar da hakan zai haifar ba karama ba ce in ji wani dan yankin Mahe Abubakar.
Kungiyar wadda ta alaka kan ta da addini ta na karbar zakka da haraji tare da kwasar dabbobin jama’a har sai sun biya, haka ma sun haramta sauraren kida domin suna yin bulala ga wadanda ke sauraren kida kamar yadda wani mazaunin ya bayyana.
Tun da farko dai Mataimakin Gwamnan Sakkwato, Idris Muhammad Danchadi ya bayyana cewar ‘yan kungiyar wadda ke ikirarin jihadi suna yawo ne da manyan makama a kananan hukumomin kuma babbar barazana ce ga al’umma, don haka ya bukaci hukumomin tsaro su gaggauta murkushe su.
A cewar Barista Bulama Burkati wanda ya jima yana bincike kan ayyukan Boko- Haram kungiyar Lakurawa ba sabuwar kungiya ba ce kamar yadda jami’an tsaro ke bayyanawa.
Ya ce kungiyar tun a 2018, ta shigo kasar nan ta Nijar kuma yanzu haka suna leken asiirin garuruwa da cibiyoyin jami’an soji a Arewa- Maso- Yamma domin gudanar da hare- haren su.
A makon jiya, daraktan yada labarai na Hedikwatar tsaro, Manjo Janar Edwin Buba ya bayyana cewar kungiyar ta samo asali ne daga Jamhuriyar Nijar a dalilin juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.
Burkati ya bayyana cewar baya ga mallakar manyan makamai masu hadarin gaske, mayakan suna amfani da jirgi maras matuki domin sa idanu kan cibiyoyin sojoji da garuruwa, don haka ya ce akwai bukatar daukar kalubalen matsalar tsaro a yankin da ‘yan bindigar daji suka riga suka kassara da matukar muhimmanci.
“Ba su da bambancin akida da Boko- Haram, illa kawai sun bayyanar da kan su kamar jami’an ‘yan sanda, sun yi ikirarin ba su son kashe jama’a, sun ce kawai suna yakar gwamnati da cibiyoyinta, wanda hakan ya fallasa tsattsaurar akidarsu ta tayar da rikici.
“Sai dai abin farin ciki shine bincike na ya nuna ya zuwa yanzu ba su samu karbuwa ga jama’a ba, ban samu misalin mutanen karkara da suka shiga cikinsu ba, har yanzu ‘yan kasar waje ne amma suna da yawan gaske a bisa ga bayanin da na samu.”
Kungiyar dattawan Arewa na kan gaba wajen nuna damuwa kan kungiyar tare da bukatar daukar matakin yakar su tare da gargadin cewar idan har har ba a dakatar da su daga samun karfin iko a Arewa-maso Yamma ba to za su iya tilasta rufe makarantu da asibitoci.
Mataimaki na musamman ga shuagaban karamar hukumar Tangaza kan harkokin tsaro, Gazali Aliyu Rakah ya bayyana cewar babbar matsalar da suke fuskanta a yanzu shine, ‘yan kungiyar sun fara kwace bindigogi a hannun dakarun tsaron da gwamnatin Sakkwato ta kafa domin yakar ‘yan ta’adda.
Ya kuma ce kungiyar na da karfin da tuni sun tilatawa barayin daji su bi su idan ba haka ba, su kore su daga daji wanda shine ma dalilin da yasa hare- haren kisan gilla da ayyukan barayin daji ke yi ya yi sauki a wannan yankin.
A ra’ayin Hassan Jabbi a karamar hukumar Gudu ya bayyana cewar bayyanar kungiyar ba karamin hadari ba ne ga al’ummarsu wadanda a tsayin shekaru ‘yan bindigar daji na yi masu kisan gilla.
Shi kuwa Iro Bashar a Tangaza cewa ya yi da farko ba su dauki kungiyar a matsayin barazana ba, domin ba su da yawa amma bisa ga abubuwan da suka fito fili a baya da yawan da suke da shi a yanzu ya nuna lallai kungiyar ta fi ta barayin dajin da aka sani hadari kwarai da gaske.