Wasu karin ‘yan Nijeriya da suka makale a kasar Sudan sun isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja daga kasar Sudan da yaki ya daidaita.
Jirgin saman Tarco Aviation dauke da mutane 126, dukkansu dalibai daga Sudan, ya isa da karfe 12:25 na rana.
- Amurka Ta Kau Da Kai Daga Yara ‘Yan Kwadago Cikin Shekaru Sama Da 200
- Za A Tafka Mamakon Ruwan Sama A Arewa A Kwanaki Masu Zuwa —NiMet
Kawo yanzu dai babu wani rahoto na asarar rai na dan Nijeriya.
Da isar wadanda suka dawo, jami’an gwamnati ne suka tarbe su.
Jami’an NEMA ne suka tarbe su tare da NIDCOM; Ma’aikatar Agaji, Ma’aikatar Harkokin Waje; da Hukumar Shige da Fice ta Kasa.
Sauran wadanda suka tarbe su sun hada da jami’an ‘yan sandan Nijeriya, hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) da sojoji.
Ya zuwa yanzu, sama da ‘yan Nijeriya 2,000 ne aka kwashe tun bayan barkewar yakin a kasar da ke Arewacin Afirka.
A cewar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta NEMA, kimanin ‘yan Nijeriya 500 ne kawo yanzu a Sudan suke jiran a kwashe su.
Wannan ita ce jigila ta tara da jirgin saman Tarco Aviation ya yi kawo yanzu.
A ranar Laraba ne gwamnatin Nijeriya ta kwaso ‘yan Nijeriya 138 daga kasar Sudan da ke Arewacin Afirka da tashe-tashen hankula daga wasu manyan hafsoshin soja biyu masu adawa da juna suka yi.
Ya zuwa yanzu dai jiragen sama na 11 ne suka kwaso ‘yan Nijeriya daga kasar Sudan, inda hukumar NEMA ta ce kawo yanzu an kwashe maza da mata da yara da mata masu juna biyu tun bayan barkewar yakin.