Abubuwan Bukata:
- Murhu
- Â Kasko
- Matsami
- Â Kwando
- Â Mazubi
- Wuka
- Â Ruwa da sauransu.
Kayan Hadi
- Â Attarugu
- Â Mai
- Danyar Citta/Garin Citta
- Albasa
- Â Kori
- Tafarnuwa Danya/Gari
- KayanKamshi
- Â Dandano
- Â Dakakken barkono
- Â Da sauransu.
Yadda ake soya Naman
Da farkoUwargidada Amarya za su tanadi kayan aiki a kusa. Da zarar an shigo miki da nama wanda aka fara shigowa da shi to shi za ki fara kokarin yankawa, idan nama ne ki fara yankashi ba tare da lokaci ya kure miki ba, ki hada wutarki ta hadu, daman kaskonki na kusa, sai ki wanke naman da kika yanka ki zuba a ciki.
Wasu ba sa wanke naman sai su zuba a haka, Uwargida da Amarya yana da kyau a samu a wanke shi ko dan tsaftace girki da kuma kare kai daga wasu kananun kwayoyin cututtukan da idanuwa basa iya gani sai an haska a abin haskawa na bature.
Wanke naman zai taimaka miki wajen rashin jin kasa-kasa a ya yin da aka zo taunawa, wasu na kin wankewa sabida ruwan jikinsa zai yawa idan ana dafawa, wasu kuma sabida wasu dalilai nasu na daban, toh idan ana gudun kada ruwa ya yi yawa za a iya tsaneshi a kwalauda in ya tsanu sai a juye a kaskon.
Bayan an zuba a Kasko sai a dora akan wuta, sannan a kawo Maidandano a zuba dai-dai yadda ake ganin zai ji, wasu suna iya hade-hade na dandano kala-kala su zuba ciki dan karin zakin nama, sai a kawo gishiri a zuba shi ma dai-dai misali yadda ba zai yawa ko kadan ba, a zuba kayan kamshi, da garin citta, danyar citta ma a jajjaga a zuba ruwa kadan a dan murje sai a tsiyaya ruwan a cikin naman, yana kara kamshi da dandano mai dadi.
A kawo garin tafarnuwa da ita kanta danyar tafarnuwar wadda aka jajjaga a zuba itama in aka hada biyu tana kara dadi sosai a girki in ma daya aka samu shikkenan ba lallai sai bibbiyun ba, a kara da sauran kayan kamshi wanda ake da su ko ake tunanin za su yi kamshi sosai kuma za su kore karni. Sai a kawo attarugu da aka jajjaga a zuba a ciki zai taimaka wajen kamshi da kuma karuwar dadin naman bayan an soya shi ba zai yaji ba sai dai in an tauna za a ji dadin dandanon sosai, a kawo Albasa a zuba a ciki, sannan a rufe.
Idan kuma kayan ciki aka fara shigowa da shi sai a wanke su sosai musamman abubuwan da aka san akwai kashi tare da su, irin su hanji, bargo, zanin mahaukaciya kamar dai yadda Hausawa ke fada, da dai sauransu.
A buda shi sosai falle-falle a wanke a tabbatar ya wanku, shima hanjin a tabbatar cikinsa ya wanku babu kashi, sabida idan aka soya ba tare da ya wanku ba zai yi daci naman, toh a wanke shi sosai, fatar da take da datti a daye dan yana makalewa, akwai abinda ake kira da Kaska a jikin naman musamman kayan ciki na rago a ciki ake samu za a gansu a makale kamar kwarika toh! a samu a fitar da shi daga jiki, komai ya gyaru ya yi tsaf!.
Za a hada masa kayan hadi kamar yadda aka hadawa nama, sai dai shi kayan ciki baya son gishiri sosai sai a kula wajen zubawa dan kar ya yi yawa.
Galibi kayan ciki ba a fiya jiran dorashi a murhu ba, akan dorashi a ainahin abin girki kamar Risho, Gas, Mangal da sauransu, kuma an fi fara dafashi sabida saurin lalacewa. Bayan an dora nama Idan ya dauki wasu mintuna biyar ko goma sai a bude naman a duba shi a juya sabida kayan dandanon da aka zuba dana kamshi su gauraya ko ina ciki sai a kara rufewa.
A haka har dai ya dahu, wasu idan suna son su yi sauri su gama dafawa ko kuma idan sun ji naman yana da tauri kamar masu soke Rakumi, suna saka ‘Paracetamol’ ko su jefa kusa a ciki sabida ya yi saurin dawuwa.
Toh! Idan aka saka ‘Paracetamol’ magani ne amma kuma an kashe amfaninsa sakamakon dafa shi da aka yi, memakon a samu abin da ake so sai kuma ya haifar da wata matsalar ta daban, dan haka yana da kyau a kula da saka ire-iren wadannan abubuwa, idan aka bi komai a tsanake toh za a yi aikin cikin nutsuwa da kuma tsafta ba tare da an damalmale gida gaba daya an rasa wajen tsugunawa ba.
Idan naman ya dawu in yana da kitse za a ga mai sosai a ciki idan kuma ba shida mai ma tun a lokacin za a gane sai a sauke wannan kaskon a kwashe naman a wanke kaskon idan ya kama kenan, bayan an wanke sai a mayar da naman ciki tare da wannan man da daya fara fitowa a saka kitse zai narke shikkenan kin hada man suyarki sai ki runka diba kina soyawa.
Idan kuma ba shi da mai sai ki sami mai ki zuba a kaskon, ki yanka albasa ya soyu sai ki kwashe albasar ki zuba naman ki rinka soyawa har ki gama gaba daya.
Idan kika gama bayan ya tsane daman kin daka barkononki ya ji mai dadi sai ki zuba a ciki ki hautsina ko ina ya biyu, wasu kuma suna saka yajin kafin su soya bayan an tafasa naman sai a zuba a hautsina, shikkenan. Idan ana son a ajjiye nama kuma ba a so ya lalace sai a zuba shi a abu mai fadi kamar faranti kuma a tabbatar ya soyu, sai a baza shi ya sha iska wanda ake son ajjiyewa kenan.