ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, November 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Suyar Naman Sallah Ta Musamman

by Bilkisu Tijjani
1 year ago
Sallah

Masu karatu ba tare da bata lokaci ba saboda yadda shirye-shiryen bikin babbar sallar bana suka kankama, zan kawo yadda za a yi suyar naman layya ta musamman wanda iyali za su ci su ji dadi.

Abubuwan Bukata:

• Murhu • Kasko • Matsami • Kwando • Mazubi • Wuka • Ruwa da sauransu.

ADVERTISEMENT

Kayan Hadi: Attaruhu • Mai • Danyar Citta/ Garin Citta •Albasa • Kori •Tafarnuwa Danya/Gari • Kayan Kamshi • Dandano • Dakakken barkono da sauransu.

  • Hilda Bassey: ‘Yar Nijeriya Da Ta Kafa Tarihi A Fannin Girki A Duniya
  • An Yi Hasashen Kone Gas Na Girki Na Naira Tiriliyan 1.5 A Nijeriya Badi

Yadda za soya Naman

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ake Miyar Margi

Yadda Ake Alkaki

Da farko uwar gida da Amarya za su tanadi kayan aiki a kusa. Da zarar an shigo miki da nama wanda aka fara shigowa da shi to shi za ki fara kokarin yankawa, idan nama ne ki fara yanka shi ba tare da lokaci ya kure miki ba, ki hada wutarki ta hadu, daman kaskonki na kusa, sai ki wanke naman da kika yanka ki zuba a ciki. Wasu basa wanke naman sai su zuba a haka, Uwargida da Amarya yana da kyau a samu a wankeshi ko dan tsaftace girki da kuma kare kai daga wasu kananun kwayoyin cututtukan da idanuwa basa iya gani sai an haska a abin haskawa na bature. Wanke naman zai taimaka miki wajen rashin jin kasa-kasa a ya yin da aka zo taunawa, wasu na kin wankewa sabida ruwan jikinsa zai yawa idan ana dafawa, wasu kuma sabida wasu dalilai nasu na daban, to idan ana gudun kada ruwa ya yi yawa za a iya tsaneshi a kwalonda in ya tsanu sai a juye a kaskon.

Bayan an zuba a Kasko sai a dora akan wuta, sannan a kawo Maidandano a zuba dai-dai yadda ake ganin zai ji, wasu suna iya hade-hade na dandano kala-kala su zuba ciki dan karin zakin nama, sai a kawo gishiri a zuba shi ma dai-dai misali yadda ba zai yawa ko kadan ba, a zuba kayan kamshi, da garin citta, danyar citta ma a jajjaga a zuba ruwa kadan a dan murje sai a tsiyaya ruwan a cikin naman, yana kara kamshi da dandano mai dadi.

A kawo garin tafarnuwa da ita kanta danyar tafarnuwar wadda aka jajjaga a zuba itama in aka hada biyu tana kara dadi sosai a girki in ma daya aka samu shikkenan ba lalai sai bibbiyun ba, a kara da sauran kayan kamshi wanda ake da su ko ake tunanin za su yi kamshi sosai kuma za su kore karni. Sai a kawo attaruhu da aka jajjaga a zuba a ciki zai taimaka wajen kamshi da kuma karuwar dadin naman bayan an soya shi ba zai yaji ba sai dai in an tauna za a ji dadin dandanon sosai, a kawo Albasa a zuba a ciki, sannan a rufe.

Idan kuma kayan ciki aka fara shigowa da shi sai a wankesu sosai musamman abubuwan da aka san akwai kashi tare da su, irin su hanji, bargo, zanin mahaukaciya kamar dai yadda Hausawa ke fada, da dai sauransu. A buda shi sosai falle-falle a wanke a tabbatar ya wanku, shima hanjin a tabbatar cikinsa ya wanku babu kashi, sabida idan aka soya ba tare da ya wanku ba zai yi daci naman, toh a wanke shi sosai, fatar da take da datti a daye dan yana makalewa, akwai abinda ake kira da Kaska a jikin naman musamman kayan ciki na rago a ciki ake samu za a gansu a makale kamar kwarika toh! a samu a fitar da shi daga jiki, komai ya gyaru ya yi tsaf!.

Za a hada masa kayan hadi kamar yadda aka hadawa nama, sai dai shi kayan ciki baya son gishiri sosai sai a kula wajen zubawa dan kar ya yi yawa. Galibi kayan ciki ba a fiya jiran dorashi a murhu ba, akan dorashi a ainahin abin girki kamar Risho, Gas, Mangal da sauransu, kuma an fi fara dafashi sabida saurin lalacewa.

Bayan an dora nama Idan ya dauki wasu mintuna biyar ko goma sai a bude naman a duba shi a juya sabida kayan dandanon da aka zuba dana kamshi su gauraya ko ina ciki sai a kara rufewa. A haka har dai ya dahu, wasu idan suna son su yi sauri su gama dafawa ko kuma idan sun ji naman yana da tauri kamar masu soke Rakumi, suna saka ‘Paracetamol’ ko su jefa kusa a ciki sabida ya yi saurin dawuwa.

Toh! Idan aka sa ‘Paracetamol’ magani ne amma kuma an kashe amfaninsa sakamakon dafa shi da aka yi, me makon a samu abinda ake so sai kuma ya haifar da wata matsalar ta daban, dan haka yana da kyau a kula da saka ire-iren wadannan abubuwa, idan aka bi komai a tsanake toh za a yi aikin cikin nutsuwa da kuma tsafta ba tare da an damalmale gida gaba daya an rasa wajen tsugunawa ba.

Idan naman ya dawu in yana da kitse za a ga mai sosai a ciki idan kuma ba shida mai ma tun a lokacin za a gane sai a sauke wannan kaskon a kwashe naman a wanke kaskon idan ya kama kenan, bayan an wanke sai a mayar da naman ciki tare da wannan man da daya fara fitowa a saka kitse zai narke shikkenan kin hada man suyarki sai ki runka diba kina soyawa. Idan kuma ba shi da mai sai ki sami mai ki zuba a kaskon, ki yanka albasa ya soyu sai ki kwashe albasar ki zuba naman ki rinka soyawa har ki gama gaba daya.

Idan kika gama bayan ya tsane daman kin daka barkononki ya ji mai dadi sai ki zuba a ciki ki hautsina ko ina ya biyu, wasu kuma suna saka yajin kafin su soya bayan an tafasa naman sai a zuba a hautsina, shikkenan. Idan ana son a ajjiye nama kuma ba a so ya lalace sai a zuba shi a abu mai fadi kamar faranti kuma a tabbatar ya soyu, sai a baza shi ya sha iska wanda ake son ajiye wa kenan.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Ake Miyar Margi
Girke-Girke

Yadda Ake Miyar Margi

November 8, 2025
Yadda Ake Alkaki
Girke-Girke

Yadda Ake Alkaki

October 19, 2025
Yadda Ake Gurasa Ta Semovita
Girke-Girke

Yadda Ake Gurasa Ta Semovita

October 12, 2025
Next Post
Sojojin Sama Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 100, ‘Yansanda Sun Ceto Mutanen Da Aka Sace A Katsina

Sojojin Sama Sun Kashe 'Yan Ta'adda 100, 'Yansanda Sun Ceto Mutanen Da Aka Sace A Katsina

LABARAI MASU NASABA

Zaɓen 2027: Jam’iyyar ADC ta Ƙaddamar Da Kwamitin Sake Fasalinta A Kaduna

Zaɓen 2027: Jam’iyyar ADC ta Ƙaddamar Da Kwamitin Sake Fasalinta A Kaduna

November 12, 2025
Sin Ta Bukaci Japan Ta Daina Yi Wa Masu Fafutukar “‘Yancin Kan Taiwan” Ingiza Mai Kantu Ruwa

Sin Ta Bukaci Japan Ta Daina Yi Wa Masu Fafutukar “‘Yancin Kan Taiwan” Ingiza Mai Kantu Ruwa

November 12, 2025
Gwamnati Ta Janye Buƙatar Amfani Da Harshen Gida Wurin Koyarwa A Makarantu 

Gwamnati Ta Janye Buƙatar Amfani Da Harshen Gida Wurin Koyarwa A Makarantu 

November 12, 2025
Peng Liyuan Da Sarauniya Letizia Ta Spain Sun Ziyarci Cibiyar Kula Da Nakasassu A Beijing

Peng Liyuan Da Sarauniya Letizia Ta Spain Sun Ziyarci Cibiyar Kula Da Nakasassu A Beijing

November 12, 2025
Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa

Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa

November 12, 2025
'yansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutane 4 Kan Zargin Fashi Da Makami A Bauchi

November 12, 2025
Ana Ci Gaba Da Raya Kasar Sin Daga Matakin Kasa Mai Sauri Zuwa Kasa Mai Inganci

Ana Ci Gaba Da Raya Kasar Sin Daga Matakin Kasa Mai Sauri Zuwa Kasa Mai Inganci

November 12, 2025
Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Matakin Amurka Na Dakatar Da Ka’idar Fadada Jerin Wadanda Kasar Ta Takaita Fitar Wa Kayayyaki

Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Matakin Amurka Na Dakatar Da Ka’idar Fadada Jerin Wadanda Kasar Ta Takaita Fitar Wa Kayayyaki

November 12, 2025
Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Nijeriya — Minista

Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Nijeriya — Minista

November 12, 2025
Majalisar Kogi Ta Dakatar Da Shugaban Ƙaramar Hukuma Bisa Zargin Rashin Ɗa’a

Majalisar Jihar Kogi Ta Dakatar Da Shugaban Ƙaramar Hukuma Kan Laifin Rashin Ɗa’a

November 12, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.