ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hilda Bassey: ‘Yar Nijeriya Da Ta Kafa Tarihi A Fannin Girki A Duniya

by Khalid Idris Doya
3 years ago
Hilda

Matashiya ‘yar Nijeriya, Hilda Bassey Effiong da aka fi sani da Hilda Baci, ta zama sarauniyar dafa abinci ta duniya bayan da ta shiga gasar dafa abinci mafi tsawo wacce ta shafe kusan awa 100 tana dafe-dafen abinci kala-kala.

Hakan ya biyo bayan wani gasa ne da Guinness ta shirya ga duk wani ko wata da zai ko ta yi girki mafi tsawon lokaci ba tare da dakatawa ba.

  • Sojoji Sun Cafke Masu Kai Wa ‘Yan Bindiga Bayanai 3 Kan Garkuwar Da Aka Yi A Kagarko
  • Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Soke Nasarar Zababben Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti

Baci wacce ‘yar kasar Nijeriya ce mai shekara 27 a duniya, an haifeta ne a karamar hukumar Nsit Ubium da ke jihar Akwa Ibom, ta yi girki na tsawon sama da kwanaki hudu ba tare da zaunawa ba, inda ta dafa abinci kala-kala har sama da dari tare da rabar wa mutane kyauta.

ADVERTISEMENT

Taken shiga gasar ta duniya shi ne ‘Dafa abinci cikin Kayyadadjen lokaci’. Ta fara girkin ne a ranar Alhamis makon jiya ta kammala ranar Litinin 15 ga Mayu, 2023 da yamma.

‘Yar Nijeriya da ta kafa tarihin nan a bangaren girki, Hilda Bassey Effiong, da aka fi sani da Hilda Baci, ta yi bayanin irin gwagwarmayar da ta sha wajen shiga a dama da ita da har ta samu nasara a bangaren dafa abinci wacce ta shafe tsawon awanni 100 tana girki.

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

Baci ta kammala karatunta ne a sashin nazarin ilimin zamantakewa daga jami’ar Madonna wacce ta fito daga gasar dafa abinci na tsawon awa 100, ta gode wa Allah da ya taimaketa ta cimma wannan nasarar da iyayenta da ‘yan uwanta.

Ta ce, ana gaf da karaya bayan shiga gasar, sannan, ta karar da dukkanin kuzarin jikinta da zai ba ta karfin guiwar cigaba, amma duk da hakan ta jure ta cigaba har sai da ta cimma nasara.

Ta ce, “Ina matukar godiya wa Allah. Na kusa sarewa a wannan gasar sa’o’i shida bayan da na fara a ranar Alhamis (Makon jiya), don na gaji kuma ba zan iya cigaba ba, amma mahaifiyata ta karfafeni ta kara min kumaji domin ta tsaya a tare da ni na tsawon awanni 14 hakan ya karfafa min guiwa matuka. Ina kan wannan matakin nasarar ne saboda goyon bayanku da na mahaifiyata.

“Ina son na shaida muku dukkaninku cewa kowani irin mafarki na iya zama gaskiya, na shirya wannan samun wannan nasarar tun shekaru biyar da suka gabata, hakan ya zama cikin mafarkina, amma ban iya yin hakan wancan lokacin ba, amma yau ga shi na iya yi dukka saboda ku. Ku nace kan mafarkinku wata rana zai zama gaskiya.”

Hilda Baci ‘My Food My Hilda’ ta lashe gasar dafa abinci na Guinness Book of Records, da ta shiga fagen dafa abinci na tsawon awa 100, lamarin da ya bai wa jama’a da dama mamaki matuka da farkar da dumbin matasa.

Masu kallon wannan al’amarin na ban mamaki da sha’awa na gasar abinci wanda aka nada a faifayin dauka, sun nuna bajintar Hilda a matsayin abun mamaki matuka gaya.

Hilda mai shekara 27, yanzu ta kafa babban tarihin wacce ta fi kowa jimawa a fagen dafa abinci.

Da take shelanta nasarar Baci na dafa abinci na tsawon awannni 96 zuwa 100 zuwa ranar Litinin din da ta gabata, babbar kawarta ta wallafa a shafin Instagram @ama_reginald cewa, “Baci ta kusan kaiwa awa 100 tana girki.”

Zuwa ranar Litnin da karfe 7:00pm, Baci ta kai awanni 99 a dakin dafa abinci, lamarin da ya kaita kwace ragamar wannan kambun a hannun wata ‘yar kasar India, Lata Tondon da ta zama tauraruwar dafa abinci na duniya a shekarar 2019.

Tata Tondon ‘yar kasar Indiya ce take rike da kambun bayan da ta shafe sa’o’i 87 da mintuna 45 a shekarar 2019 tana girki.

Masu shirya gasar ‘Guiness World Record’ sun ce, kafin su amince da mutum ya samu nasarar sai ya gabatar musu da kwararan hujjojin lashe gasar da dukkanin matakan da aka gindaya.

Daga cikin abubuwan da ake alakari da su shine na farko mai bukatar shiga gasar zai gabatar da bukatar nuna sha’awar hakan da gabatar da kansa, zai/za ta yi girki na tsawon kwanaki 4 ba tsayawa; dole mai shiga gasar ya yi girki mafi tsawo ba tare da zaunawa ba, wanda ya fi yin girki na tsawon lokaci bai sare ba shine ke da kambun.

Kazalika, babu shan wasu kwayoyin kara kuzari ko na karfin jiki yayin shiga gasar ba; mai shiga gasar na da damar cin abinci, shan ruwa ko ruwan ‘ya’yan itace, da shan glucose.

Ita dai Baci ta shiga gasar ne daga wurin shakatawa na ‘Amore Gardens’ da ke Lekki, Jihar Legas, Nijeriya. ta yi girki safe da dare da rana na tsawon darare 4 ba tare da yin barci ba. Ta kan samu hutun minti 5 a kowani awa. Ta na kwashe mintuna 30 a cikin motar asibiti da ke kusa da ita, inda za ta iya yin barci, ta yi amfani da dakin wanka, sannan ta sami tantancewar likita ko duba lafiyar ta daga tawagar likitoci.

Kazalika, duk abin da ta dafa tana raba wa mutanen da ke wurin kyauta ba tare da sayar da abincin ba. Ta kan dafa abinci daban-daban lokaci guda. Tana da ‘yancin dafa duk abincin da take so. Babu takurawa kan girkin da ta iya da wanda ba ta iya ba.

Kowane abinci da aka dafa da kowane farantin da aka ba da shi ana rubuta shi. Ta dafa abinci sama da kala 115 kawo yanzu.

Kuma dukkanin yadda mai shiga gasar ya kasance to zai tura kai tsaye wa masu kula da gasar don haka ne ta kafa wannan tarihin.

Sai dai, masu shirya gasar sun ce, bayan mutum ya tura musu daukan hujjojinsa, to za su shafe tsawon mako 12 suna bibiya da tantance abubuwan da aka turo musu kafin daga bisani su amince da shi ko kin amincewa da shi.

  • Ta Kasance Jaruma, Mai Aiki Tukuru – Cewar Ahlinta

Iyalanta da makusantansa tauraruwar girki ‘yar Nijeriya, Hida Baci, sun misaltata a matsayin wacce ta bada mamaki matuka wajen zage damtse da yin aiki tukuru wajen zama a wannan tarihin na duniya baki daya, sun ce, ta yi aiki sosai ta kuma jure.

Daya daga cikin ahlinta, Chisom Nwafor, ta shaida wa LEADERSHIP cewa, ‘yar uwan tasu tana da hali mai kyau, tana faran-faran da kowa, kuma mai son nasara da sanya abun da ta sa a gaba da naci da dagewa.

Chisholm wacce ita ma take dafa abinci a Calabar Pot, kuma tana safaran abinci ma ta yanar gizo, ta ce, Hilda ta fara dafa abinci tsawon shekaru kuma tana matukar sha’awar abun da take yi, “Na yi matukar farin ciki domin ta cimma nasara kan mafarkinta na tsawon lokaci. Ta jima da wannan burin nata,” ta shaida.

  • Tabbas Allah Mai Iko Ne Kan Komai, A Cewar Mahaifiyar Hilda

A bangaren mahaifiyar Hilda kuwa, Misis Lynda Ndukwe, cike take da murna da cigaba da godiya da jinjina ga Allah. Ta ce, ba za ta daina godiya ga Allah ba da ya dafa mata a kowani lokaci.

Ta ce, diyarta ta kasance wacce ta canza musu tarihi ta hanyar kafa tarihin da za su jima suna alfahari da ita, ta ce mafarki ne ya zama gaskiya domin diyar nata ta cimma da wannan burin a cikin ranta.

Sai ta gode wa fitaccen malamin nan, Fasto Jerry Eze, wacce ta ce ita kanta diyar nata ma za ta kasance mai mai yi masa yabo.

Ndukwe wacce ita ce shugaban wurin dafa abinci na Calabar Pot ta kasance jigon taimaka wa diyarta tun lokacin da ta fara buga-bugar shiga gasar har zuwa lokacin da ta yi nasara. An yi ta ganota a yanar gizo tana godiya wa Allah.

Shugaba Buhari, Osinbajo, Gwamnoni da wasu fitattun mutane sun taya Sarauniyar Girki, Hilda Barci Murna

Har-ila-yau, shugaban kasa Muhamadu Buhari, ya taya sarauniyar dafa abinci, Hilda Bassey Effiong murnar lashe gasar dafa abinci mafi tsawo na Guinness, da cewa ta daukaka kimar Nijeriya.

Buhari a sanarwar da kakakinsa Femi Adesina ya fitar, ya yaba da kwazo, himma, azama da sa’ayin Hilda, yana mai cewa hakan wani mataki ne da zai kara kyautata tattalin arziki.

Buhari ya ce, Hilda wacce ta kasance mai gudanar da wurin sayar da abinci a Legas, ta koyar da wasu sosai kan yadda za su tsayu da kafafunsu yanzu kuma ta samu tagomashi a duniya baki daya.

Buhari ya nuna kwarin guiwarsa na cewa yadda Hilda ta dage wajen cimma burinta, hakan zai farkar da ‘yan Nijeriya da dama su ma su dumfari mafarkinsu ta yadda za su ga sun cimma nasara domin rayuwarsu take ingantuwa.

Kazalika, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, gwamnan Legas, zababben shugaban kasa Asiwajo Bola Ahmed Tinubu da sauran fitattun mutanen Nijeriya sun nuna farin cikinsu da taya Hilda murna tare da mata fatan cewa matasa da dama za su moreta.

Hilda
Khalid Idris Doya
+ postsBio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    An Kama Mutane 5 Da Sassan Jikin Ɗan’Adam Za Su Yi Tsafi A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan Bauchi, Bala Jibrin, Ya Fice Daga APC Kan Zargin Ɗoki-ɗora
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    ‘Yansanda Sun Cafke Tsoho Mai Shekara 70 Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 8 Fyaɗe A Bauchi

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
Sharhi: Kasashen Duniya Za Su Gano Amsa In Sun Kwatanta Tarukan Koli Na Xi’an Da Hiroshima

Sharhi: Kasashen Duniya Za Su Gano Amsa In Sun Kwatanta Tarukan Koli Na Xi’an Da Hiroshima

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.