Rundunar Sojin saman Nijeriya ta tabbatar da kashe ‘yan ta’adda sama da 80 tare da lalata babura 45 a wani harin da ta kai ta sama a ƙauyen Gidan Kare da ke jihar Katsina.
An kai harin ne a ranar 15 ga watan Yunin 2024, bayan wasu bayanan sirri sun nuna cewa sama da ‘yan ta’adda 100 ne ke kona gidaje tare da shirin ƙara kai hare-hare a wasu ƙauyukan da ke kusa.
An hango ‘yan ta’addan suna taruwa a wani wuri da ke kusa da ƙauyen Gidan Kare da kuma sansanin Kuka Shidda kafin rundunar Sojojin ta NAF ta far musu, lamarin da ya kawo ƙarshen ayyukansu.
- Sojoji Na Kan Bakarsu Na Tabbatar Da Tsaron Kasa – Shugaban Tsaro
- An Tafka Gumurzu, Sojoji Sun Kashe Ƴan Boko Haram Da Yawa, Wasu Sun Miƙa Wuya
Iya Mashal Edward Gabkwet ya bayyana cewa ‘yan ta’addan na da alaƙa da manyan ƴan ta’adda irinsu Yusuf Yellow da Rabe Imani.
Hare-haren ta sama, wanda aka ba da izini bayan an kiyayewa kuskure, ya samu gagarumar nasarar kawar da barazanar ƴan ta’addan daga yankin.
Wannan farmakin dai na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na kakkabe hanyoyin sadarwar ‘yan ta’adda a yankin da kuma hana kai hare-hare a nan gaba.
Shugaban hafsan sojin sama, Iya Mashal Hassan Abubakar, ya yabawa rundunar Sojin sama da sauran jami’an tsaro bisa haɗin kan da suke yi wajen yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso yamma.
A ziyarar da ya kai sansanin ‘Forward Operating Base’ mai lamba 213 da ke Katsina, ya jaddada muhimmancin ci gaba da sadaukarwar da suke da shi, ya kuma ƙaddamar da sabbin na’urori na filayen jiragen sama domin inganta ayyukansu.
Wannan yunƙurin wani ɓangare ne na dabarun tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali na dogon lokaci a yankin.