A wadannan kwanaki na ga yadda wasu kafofin watsa labaru na kasashen yamma suke ruruta cewa, wai kasar Sin ta gamu da cikas a fannin farfado da tattalin arziki, abun da zai haifar da illa ga yanayin tattalin arziki na kasashen Afirka. Ko abun haka yake?
Hakika, ko da yake kasar Sin na bukatar daidaita wasu matsaloli irinsu samun bangaren masana’antu dake samar da kayayyaki fiye da yadda ake bukata, da yanayin rashin tabbas a kasuwannin kasa da kasa, amma duk da haka, tattalin arzikinta na cikin wani yanayi mai armashi. Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, a rubu’i 3 na farkon bana, jimilar kudin kayayyaki da ayyukan hidima da aka samar (GDP) a kasar Sin ta karu da kashi 5.2%, bisa makamancin lokacin bara. Kana a nasu bangare, bankin duniya, da asusun ba da lamuni na duniya (IMF), suna da yakinin cewa kasar Sin za ta iya cimma burinta na samun karuwar GDP ta kashi 5% a shekarar da muke ciki. Ban da haka asusun IMF ya ce, kasar Sin za ta samar da gudunmowa ga karuwar GDPn duniya da ta kai kashi 22.6%, cikin shekaru 5 masu zuwa.
- Sin Ta Gudanar Da Taron Kolin Ayyukan Raya Tattalin Arziki
- Babban Jami’in Jaridar Aljeriya: BRI Ta Inganta Hakkin Dan Adam A Kasashen Dake Raya Shawarar
Sa’an nan a nasu bangare, kasashen Afirka ma suna cikin wani yanayi mai kyau ta fuskar raya tattalin arziki. A cewar wani rahoton da gungun kwararrun ilmin tattalin arziki na kasa da kasa na EIU ya gabatar a kwanan baya, nahiyar Afirka za ta bi sahun Asiya, inda za ta zama yanki na 2 mafi saurin karuwar tattalin arziki. Bayanai na cewa karuwar GDPn nahiyar za ta tashi daga kashi 2.6% a shekarar 2023 zuwa kashi 3.2% a shekarar 2024, jimillar da za ta haura matsakaicin matsayi na duniya. Saboda haka, idan an kwatanta da sauran yankunan duniya, ko kasar Sin, ko ma kasashen Afirka, ba za a ce farfadowar tattalin arzikinsu na tafiyar hawainiya ba.
Sai dai idan an kwatanta da yadda kasashen suke kafin barkewar annobar COVID-19, misali a shekarar 2019, to, za a iya ganin yanayi na raguwa a fannin saurin karuwar tattalin arziki, da na jimillar ciniki, da dai sauransu. Wannan ba abun ban mamaki ba ne, ganin yadda annoba, da rikicin siyasa, da hauhawar farashin kayayyaki, gami da sauran dalilai, suka haddasa koma bayan tattalin arzikin duniya baki daya, cikin wadancan shekaru, wanda ya shafi dukkan kasashen duniya daban daban. Hakika yanayin tattalin arziki kullum yana sauyawa. Abun da ya kamata mu yi, shi ne, a hada kai a kokarin tinkarar kalubaloli, don ganin an farfado da tattalin arizkin duniya cikin sauri. Sai dai dole ne mu lura da wani yunkurin da ake yi, wato haifar da rarrabuwa a duniya zuwa wasu gungu-gungu, da yanke huldar ciniki a tsakaninsu.
A cewar mataimakiyar darektan asusun IMF, Gita Gopinath, an sanya matakan takunkumi kimanin 3000 a duniya a bara, jimillar da ta ninka ta shekarar 2019 har ninki 3. Ta kuma yi gargadin cewa, idan an raba tattalin arzikin duniya zuwa mabambantan gidaje, to, GDPn duniya ka iya raguwa da kashi 2.5% zuwa 7%. A nata bangare, kasar Sin ma ba ta yarda da yunkuri na mai da bambancin ra’ayi a fannin siyasa ya zama fito-na-fito ta fuskar tattalin arziki ba. Dangane da matakin katse huldar ciniki da kasar Amurka da wasu kasashe su kan dauka ta hanyar fakewa da maganar tsaro, kasar Sin ta sha jaddadawa cewa, rashin hadin kai da ma ci gaba su ne suke haddasa rashin tsaro da kwanciyar hankali. Don haka, kamata ya yi, kasashe daban daban su yi kokarin hadin gwiwa da juna don tabbatar da moriyarsu ta bai daya, ganin yadda suke dogaro da juna a fannin raya tattalin arziki.
Sai dai idan muka kalli ra’ayin kasar Amurka, za mu ga cewa ba ta son hada kai da sauran kasashe. Ko da yake tattalin arzikin duniya na fuskantar wani yanayi na koma baya, amma kasar Amurka na ci gaba da kokarin kwatan dukiyoyi a duniya ta hanyar nuna fin karfi, don neman kare matsayinta na babakere a duniya. Idan kamfanin wata kasa ya sha gaban nasa ta fannin wasu fasahohi, to, sai Amurka ta nemi wani dalili don yanke masa hukunci ko kakaba masa takunkumi na kashin kai. Idan wata kasa ta ci kyakkyawar riba daga tsarin masana’antun duniya, to, Amurka za ta yi kokarin ganin ta raba kasar da tsarin. Idan an ta da yaki a wasu wurare, to, kasar za ta kara rura wuta don sanya yaki ya dore, ta yadda za ta iya sayar da dimbin makaman da ta kera don tabbatar da moriyar kanta. Gaskiya kasar Amurka ta cika son kai. Saboda haka, bai kamata a ce akwai fito-na-fito tsakanin rukunonin kasashe a duniya ba. Kawai ana samun rikici a fannin moriya tsakanin kasar Amurka da mafi yawan kasashen duniya. Sai dai akwai wasu kasashe kalilan da suke hada moriyarsu da ta kasar Amurka tun tuni, don haka ba yadda za su yi, sai su bi umarninta.
Babu shakka, galibin kasashen duniya ba su son yin watsi da damar samun farfadowar tattalin arzikin duniya don goyon bayan yunkurin katse huldar ciniki da kasar Amurka ke jagorantar, saboda sun san cewa akwai bukatar hadin gwiwar kasashe daban daban, illa dai ana son ganin tattalin arzikin daukacin duniya ya farfado cikin sauri. (Bello Wang)