Kamar yadda aka sani, kamfanin siminti na BUA karkashin jagorancin Alhaji Abdussamad Rabiu ya sanar da cewa, nan gaba kadan zai rage farashin siminti a fadin kasar daga naira 5,500 a kan kowanne buhu zuwa Naira 3,000. Ya ce, sun yanke wannan shawarar ne don yin haka tamkar nuna goyon bayansu ga kudurin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na samar da isssun gidaje ga al’umma Nijeriya da kuma hankoron ganin an samar da ayyukan yi ga dinbin matasanmu.
Tabbas wannan shirin zai taikama wa rayuwwar talakan Nijeriya, don samar da siminti mai sauki zai zaburar da harkar kwangila na gine-gine a fadin tarayya Nijeriya abin da kuma zai kai ga daukar masu kananan sana’o’i da leburori da dama aiki.
- An Gabatar Da Sanarwar Taron Kula Da Harkokin Masana’antu Da Kasuwanci Bisa Doka
- Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Sabbin Shirye-shiryen Inganta Tsaro A Jihar Kaduna
Babu shakka in har leburori da birkila, da masu walda da fulamba da sauran wadanda suke gudanar da sana’ar su da ta shafi bangaren gine-gine suka samu abin yi, al’umma da suka shafe su za su samu abinci mutane za su samu karin walwala.
Sai dai tambayar da mutane da dama suke yi, shi ne wai shin yaushe za a fara cin gajiyar wannan rage farashin? Shugaban kamfanin BUA, Alhaji Abudussamad Rabiu ya ce, wannan Shirin ya danganta ne ga shirinnsu na bude wasu sabbin kamfanoni biyu da suke sa ran za su rinka samar da tan miliyan 3 na siminti a duk mshekara wanda suke sa ran za a kamala aikin ginawa nan zuwa karshen shekara.
Sabbin kamfanonin guda biyu in har suka fara aikii za su kara yawan simintin da BUA ke samarwa zuwa tan Miliyan 17 a duk shekara wanda hakan zai mayar da kamfanin mafi girma a bangaren samar da siminti a fadin Afirka gaba daya. Shugaban kamfanin ya ce, suna sa ran cimma wanna ne saboda yadda suke samar da kayan hada simininti a cikin gida.
“Kashi 80 na kayan da muke hada siminti da su muna samu ne daga cikin gida, a kan haka muke son tallafa wa gwamnati wajen tabbatar da ganin an dawo da farashin siminti zuwa farashin da ya dace da talaka.” In ji shi.
Abdussamad Rabiu ya kuma bayyana cewa, ana sa ran shugaban kasa Tinubu zai kaddamar da sabbin kamfanin nan gaba a cikin wannan shekarar ta yadda abin da muke samarwa zai kai tan miliyan 17 a duk shekara.
Masu sharhi a kan harkokin yau da kullum sun nuna jin dadinsu a kan wannan matakin suna mai cewa, yin hakan zai zaburar da tattalin arzikin kasa, musamman a bangaren gine-gine na kamfanoni da mutane daidaiku.
Wannan ragin kuma zai taimaki al’umma musamman masu gidaje da masu haya don zai kai ga rage kudin haya a nan gaba.
Kotu Da “yansanda