“A cikin shekaru 25 da suka gabata, a karkashin cikakken goyon baya daga kasar uwa, da kuma kokarin hadin gwiwa da gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, da ma dukkan bangarorin al’ummar yankin suke yi, manufar ‘kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu’ ta samu nasarar da aka sani a Hong Kong. ”
A ranar 1 ga watan Yuli, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da muhimmin jawabi a wajen bikin cika shekaru 25 da dawowar Hong Kong kasar Sin, da kuma bikin rantsuwar kama aiki ta gwamnatin yankin musamman na Hong Kong karo na shida, inda ya nuna yabo sosai kan yadda ake gudanar da manufar “kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu” a Hong Kong.
Da karfe 0:00 na ranar 1 ga watan Yulin shekarar 1997, gwamnatin kasar Sin ta dawo da ikon mallakar yankin Hong Kong, kuma a hukumance aka kaddamar da sabon tsarin siyasa na “kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu”.
A cikin shekaru 25 da suka gabata, yankin Hong Kong ya shawo kan kalubale daban-daban, kuma an tabbatar da matsayinsa na cibiyar hada-hadar kudi, da ta jigilar kayayyaki, da ta cinikayya ta kasa da kasa, kana mazauna Hong Kong na samun ikon demokuradiyya, da ‘yancin kai da ba a taba ganin irinsa ba, kuma an kyautata jin dadin jama’a sosai.
Ga misalin, jimillar GDP na Hong Kong, da matsakaicin GDP na kowane mutum sun karu, daga dalar HK tiriliyan 1.37 da dalar HK dubu 192 a shekarar 1997, zuwa dalar HK tiriliyan 2.86 da dalar HK dubu 387 a shekarar 2021. Kaza lika yawan kudin musaya da aka tanada ya ninka sau 5 bisa na shekaru 25 da suka gabata.
Hong Kong ya samu gagarumar nasara a cikin shekaru 25 da dawowarsa kasar Sin, wanda ke nuna cewa, manufar “kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu” ta Hong Kong ta samu gagarumar nasara, a cikin shekaru 25 da dawowar yankin, kana hakan ya nuna cewa, manufar “kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu” ta jure duddubawa daga yunkurin aikatawa, wadda kuma ke dacewa da moriyar kasa, da babbar moriyar al’umma, da babbar moriyar Hong Kong da Macau, kuma hakan ya samu goyon baya daga wajen Sinawa fiye da biliyan 1.4, da goyon bayan bai daya na mazauna Hong Kong da Macau, har ma ya samu amincewar kasashen duniya baki daya. “Irin wannan tsarin mai kyau, babu wani dalili na canza shi, kuma dole ne a gudanar da shi cikin dogon lokaci!” (Mai fassara: Bilkisu Xin)