Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta yi kira da a karo mata sojojin sa-kai da za su taimaka mata wajen kare kasar daga hare-haren masu ikirarin jihadi.
Gwamnatin ta yi kiran ne bayan rahotanni da aka fitar a makon da ya gabata cewa an kashe sojoji kusan 150 a lokacin da wasu mayaka da ke da alaka da kungiyar Al Ka’eda suka kai hari kan wani jerin gwanon motocin sojoji a yankin Gabashin kasar.
- Shugaban Seychelles: Raya Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Na Da Makoma Mai Haske
- Minista Ya Buƙaci Kafafen Yaɗa Labarai Na Duniya Su Riƙa Bayar Da Rahoton Gaskiya Kan Nijeriya
Tun lokacin da Ibrahim Traoré, ya kwace mulki a kasar shekaru biyu da suka wuce, ya yi alkawarin inganta tsaro a fadin kasar.
Dubban fararen hula ne aka ba wa bindiga domin su bi sahun ‘yan sa-kai don kare kasar.
To amma a shekarar da muke ciki hare-haren masu ikirarin jihadi ya karu sosai a kasar.