Mataimakiyar Sakatare Janar ta Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed, ta jaddada muhimmancin magance matsalolin ta’addanci da tallafa wa al’ummomin da abin ya shafa a fadin Afirka.
Mataimakiyar ta bayyana haka ne a yayin wani taro na yaki da ta’addanci da aka gudanar a ranar Litinin, a Abuja.
- PSG Na Neman Dauko Lamine Yamal Daga Barcelona A Kan Yuro Miliyan 200
- EFCC Ta Sake Maka Emefiele A Kotu Kan Wasu Sabbin Tuhume-tuhume 4
Ofishin Mai Ba Da Shawara kan Harkokin Tsaro (ONSA) tare da hadin gwiwar ofishin yaki da ta’addanci na Majalisar Dinkin Duniya (UNOCT) ne, suka shirya taron.
Taron da aka yi wa taken ‘Karfafa Hadin Gwiwar Yanki Da Ci Gaban Cibiyoyi Don Tunkarar Barazanar Ta’addanci a Afirka’.
Amina ta kara jaddada illar ta’addanci da munanan illolin da yake haifarwa ga al’umma, musamman mata da ‘yan mata wadanda galibi su ne ke fuskantar cin zarafin ta’addanci.
Bugu da kari, ta yaba wa Nijeriya bisa kiran taron kolin don magance matsalolin mata, masu rauni, da wadanda ta’addanci ya shafa.
“Dole ne mu samar da ingantattun dabaru da za su magance wadannan kalubale, tare da mayar da hankali kan halin da mata da ‘yan mata ke ciki wadanda rashin tsaro ya shafa,” in ji ta.
Da ta ke bayyana muhimmancin saka hannun jari ga matasa, Amina ta bukaci kasashen Afirka da su samar da yanayi mai kyau don ci gabansu da wadata.
Ta kara da cewa muhimmancin taron ya wuce Nijeriya, inda ta yi kira da a yi kokarin hadin gwiwa daga kasashen Afirka a fadin nahiyar, ciki har da Ghana da Togo, domin samun ci gaba wajen yakar ta’addanci da kuma tallafa wa al’ummar da abin ya shafa.
Ta kuma bayyana takaicinta game da yadda ake yin watsi da al’amuran mata da ‘yan mata a manyan tarukan duniya.
“A manyan tarukan da shugabannin kasashen duniya ke tattaunawa, an mayar da hankali ne bisa karfafa gwiwar matasa da matakan yaki da ta’addanci, tare da kawar da matsalolin da suka shafi mata.
“Sai dai a yanzu, abin farin ciki ne ganin yadda al’amuran mata ke samun karbuwa a irin wadannan dandali,” in ji ta.