Allah ya kawo mu shekara ta 2025, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi wa ’yan kasar jawabi mai ratsa zuciya, kuma mai cike da karsashi na baiwa Sinawa kwarin gwiwa da gamsuwa a kan matsayin da kasar ta kai a yau.
A cikin jawabin nasa, shugaba Xi Jinping ya tabo batutuwa masu muhimmanci da suka hada da tattalin arziki, aikin gona, kimiyya da fasaha, al’adu, zamantakewa tsakanin al’ummar kasar Sin da kuma matsayin Sin a matsayin kasa daya.
Alal hakika, idan aka lura da wannan jawabi na Mr. Xi, za’a fahimci cewa ya yi wa kansa da daukacin Sinawa adalci. Domin kuwa ko mutum baya kaunar Allah, dole ne ya yarda cewa tattalin arzikin kasar Sin ya yi matukar bunkasa. Abin lura a nan shi ne, yawancin kasashe ba su yi la’akari da abin da bunkasuwar tattalin arziki ke haifarwa ga muhalli, musamman ta gurbata muhalli da yanayi. Amma abin burgewa a nan dangane da irin bunkasuwar tattalin arzikin da kasar Sin ta samu mai tsabta ne, ba mai gurbata mahahalli ba, sabanin irin yadda wasu kasashen ke zub da dagwalon masana’antu a cikin teku, abin da ke illa ga halittun ruwa, ko kuma fitar da hayaki mai gurbata iska dake illa ga bil adam.
Kada a manta cewa kasar Sin tana kan gaba ta fannin kera motoci masu aiki da wutar lantarki, a cikin shekara ta 2024 kadai, sama da motoci masu aiki da lantarki miliyan goma ne aka kera a kasar Sin. Bugu da kari ita kanta wutar lantarki mai tsabta ce, domin kuwa akasarinta daga hasken rana da karfin iska da ma sauran nau’o’in makamashi masu tsabta ake samunta.
Mu waiwaya bangaren kimiyya da fasaha, kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba ta fannin fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam (AI) da kuma fasahar sadarwa. Sa’an nan, a karo na farko na’urar bincike ta Chang’e 6 ta dauko samfura daga bangaren bayan duniyar wata, kana babban jirgin ruwan binciken teku na Mengxiang ya gudanar da bincike a sashen teku mai zurfi.
Idan muka koma bangaren noma kuwa, yau an wayi gari kusan daukacin abincin da Sinawa ke ci, a cikin kasar Sin ake noma shi. A shekarar 2024, adadin yawan hatsin da aka noma a kasar ya kai sama da tan miliyan 700, ba’a ma maganar kayan lambu da sauran nau’ikan ’ya’yan itace. Harkar noma dai ta yi matukar tasiri wajen fitar da mazauna yankunan karkara daga cikin kangin talauci.
Dangantaka tsakanin Sin da sauran kasashen duniya kuwa sai hamdala. Idan ba’a manta ba, a cikin shekarar da ta gabata, Sin ta tara shugabannin kasashen Afirka a birnin Beijing, domin gudanar da taron dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka. Taron dai ya samu gagarumar nasara, ba domin komai ba, sai don yadda shugabannin na Afirka suka fahimci cewa kasar Sin ba ta da wata boyayyar manufa, illa iyaka kawai domin kowa ya amfana a kuma ci moriyar juna.
Daga karshe, shugaba Xi Jinping ya kara jaddada matsayin kasarsa a kan batutuwan da suka shafi Macao, Hong Kong da kuma Taiwan, a matsayin kasa daya mai bin tsarin mulki biyu. A bayyane take kan irin ci gaban da Macao ta samu tun lokacin dawowarsa karkashin mulkin kasar Sin shekaru 25 da suka gabata. Wannan lamari ya kara kunyata masu kulla makircin ballewar Taiwan daga kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp