• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tabbatar Da Tsaro A Jihar Zamfara

- Gwamnati Ta Zuba Jami'an Tsaro A Muhimman Wurare - Sun Fara Sintiri A Manyan Hanyoyi

by Leadership Hausa
2 years ago
Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ɗauki matakin zuba jami’an tsaro a manyan hanyoyin da ke fuskantar barazanar ‘yan bindiga.

Idan ba a manta ba, a zaman Majalisar Tsaro ta Jihar Zamfara wanda aka gudanar makon da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya yi ƙorafi ga shugabannin ɓangarorin tsaro na jihar kan wasu hanyoyi da ‘yan bindiga ke cin karensu babu babbaka. Musamman hanyar Gusau zuwa Funtua; Magami zuwa Dangulbi zuwa Dan Kurmi zuwa Anka, da kuma hanyar Magami zuwa Dansadau.

  • Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Zagayen Rangadin Duba Aiyuka A Jihar Zamfara
  • Gwamna Dauda Lawal Ya Ƙaddamar Da Fara Rabon Tallafi A Jihar Zamfara

Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, a wata sanarwar manema labarai da ya fitar yau a Gusau, ya ce, zuba jami’an tsaro a hanyar Gusau zuwa Funtua da sauran hanyoyi na daga cikin shirin gwamnatin don tabbatar da kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Ya ƙara da cewa, jami’an tsaron da ke sintiri a waɗannan hanyoyi sun haɗa da sojojin ƙasa, sojojin sama da ‘yan sanda.

Ya ce: “A taron Majalisar Tsaro ta Jihar Zamfara wanda aka yi makon da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya nemi shugabannin sojoji da ‘yan sanda su tura motoci masu silken a CSK da APC domin yin sintiri a muhimman hanyoyin da ‘yan bindiga ke ta’asa.

LABARAI MASU NASABA

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

“Haka kuma gwamnan ya yi wa shugabannin jami’an tsaron alƙawarin duk wani tallafi da suke buƙata don yiwuwar aikinsu ba tare da wata tangarɗa ba.

“Cikin matakan da gwamnatin Dauda Lawal ke ɗauka don magance wannan masifa ta rashin tsaro ne ya sa ta bayar da umurnin a rufe wasu kasuwanni da ake amfani da su wurin cinikayyar shanu da tumakin sata.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba
Labarai

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta
Manyan Labarai

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin
Manyan Labarai

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Next Post
Wa Suka Fi Cancanta A Nada Ministocin Tinubu?

Kwana 100 Na Mulkin Tinubu; Da Gaske Bayan Duhu Sai Haske?

LABARAI MASU NASABA

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.