Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau Jumma’a 5 ga wata cewa, a jiya, lokacin da yake ganawa da manema labarai bisa hadin gwiwa da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, shugaba Xi Jinping ya ayyana cewa, kasar Sin za ta ba da taimakon dalar Amurka miliyan 100 ga Falasdinu, domin saukaka matsalar jin kai a zirin Gaza, da kuma tallafa mata wajen farfadowa da sake gina ta.
Lin ya ce, kasar Sin na goyon bayan tabbatar da adalci ga al’ummar Falasdinu wajen maido da hakkinsu na kasa mai ‘yanci, kuma za ta ci gaba da yin aiki tukuru tare da kasashen duniya, don tabbatar da tsagaita bude wuta mai dorewa a zirin Gaza, da sassauta yanayin jin kai a can, da warware matsalar Falasdinu a siyasance cikin hanzari bisa shawarar kafa kasashe biyu a yankin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














