ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wuta Ta Ƙone Miji, Mata Da Ƴaƴansu Ƙurmus A Katsina

by Sani Anwar
9 months ago
wuta

Wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar ranar Litinin, ta yi sanadiyar mutuwar mutum biyar tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin nairori a Ƙauyen Kofar Sauri da ke cikin birnin Katsina.

Muhammad Habibu mai shekara 35 da matarsa Fatima Muhammad da ‘ya’yansu uku, Khadija, Abubakar da Aliyu, dukkanninsu sun ƙone ƙurmus.

  • Gobara Ta Yi Ajalin Mutum 5 ‘Yan Gida Ɗaya A Jihar Katsina
  • Hukuma Ta Gargaɗi Jama’a Kan Amfani Da Wuta A Lokacin Hunturu A Kano

Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Muhammad Habibu, ma’aikaci ne a hukumar ruwa ta Jihar Katsina, har zuwa rasuwarsa.

ADVERTISEMENT

Duk da cewa, har yanzu ba a tantance ainihin musabbabin tashin gobarar ba, mazauna yankin na zargin tashin wutar a lokacin da aka dawo da wutar lantarki a yankin.

Har ila yau, gobarar ta tashi ne daga falo tare da bazuwa cikin sauri zuwa sauran ɗakuna yayin da suke tsaka da yin barci.

LABARAI MASU NASABA

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

Wani ɗan’uwan waɗanda abin ya shafa mai suna Kasim Aliyu ya ce, da misalin ƙarfe 3:00 na dare ya ji muryar wata mata daga nesa tana faɗin; “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un”, (Haƙiƙa ga Allah muke, kuma gare shi za mu koma).

Da farko, ya yi tunanin al’ada ce wadda aka saba yi, har sai zuwa ƙarfe 3:30 na dare, lokacin da ya hango wani abu mai kama da wuta na tashi.

Kasim ya ƙara da cewa, “Mai gidan, yayana ne; ubanmu ɗaya da shi, gobarar ta ƙone gidan da ne misalin ƙarfe 3:00 na dare, sai na hango wani abu a lokacin, amma ban san ko mene ne ba, har sai da aka kira ni da misalin ƙarfe 4:00 na dare, inda aka sanar da ni cewa; yayana da iyalansa baki-ɗaya sun mutu sanadiyyar gobara, Allah ya gafarta musu, ya ba su Aljannar Firdausi.

Shedun gani da ido sun bayyana cewa, duk da ƙoƙarin da maƙwabta da sauran waɗanda suka kai ɗauki suka yi, amma abin ya ci tura. Duk da dai, sun koka da yadda jami’an hukumar kashe gobara ta Jihar Katsina suka zo a makare, ba tare da kuma yin wani abin a zo a gani ba.

Wani daga cikin maƙwabtan mamacin mai suna Musa Hamza ya ce, “Ina da yaƙinin cewa, lokacin da hukumar kashe gobara ta zo, tuni mutanen gidan sun riga sun mutu, duk da cewa; sun yi iya ƙoƙarinsu wajen ganin sun kashe wutar, amma ba su iya yin nasarar ceto mamatan ba.

Shi ma, guda daga cikin maƙwabtan, Magaji Bala, ya koka kan yadda mazauna garin sukan kwana ba tare da wutar lantarki ba, sai dai yanayin yadda ake kawo wutar lantarkin, yakan haifar da ɓarna a duk lokacin da wutar ta dawo.

“Wannan lamari yana faruwa a wasu sassa na cikin birnin Katsina, a kwanakin baya ma; makamancin hakan ya kusan faruwa, don haka; akwai buƙatar yin taka-tsan-tsan a tsakanin mazauna wannan gari,” inji shi.

Da aka tuntubi babban jami’in kashe gobara na hukumar kashe gobara ta Jihar Katsina, Rabe Audi Kurmuyal, ya tabbatar da cewa; mutanensa ne suka kashe gobarar, saɓanin iƙirarin da ake yin a cewa; ƴan kwana-kwanan sun isa wajen a makare.

Haka zalika, wasu mazauna yankin sun yi zargin cewa; kamfanin rarraba wutar lantarki na (KEDCO), na ci gaba da samun taɓarɓarewa wajen samar da wutar lantarki, inda suka ce; yawan katsewar wutar lantarkin akai-akai da kuma dawo da ita ne musabbabin lalata na’urorin lantarkin.

Da take jajanta wa iyalai da abokan arziƙi da maƙwaftan waɗanda abin ya shafa, Sakatariyar Zartarwa ta Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Katsina (SEMA), Binta Hussaini Dangani, ta bayyana faruwar lamarin a matsayin wani iftila’i daga Allah SWT, sannan ta yi addu’ar Allah ya gafarta wa waɗanda suka rasu ya kuma sanya su cikin Aljanna Firdausi.

Dangani, wadda ta isa wurin mintuna kaɗan bayan faruwar lamarin, ta yi addu’ar Allah ya kawo mana ƙarshen wannan bala’i tare da bayar da tabbacin cewa, gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa iyalan waɗanda abin ya shafa. Sannan, ta shawarci mazauna garin, da su riƙa tabbatar da kashe kayan wutan lantarki a koda-yaushe kafin su kwanta barci tare da kula da harkokin da suka shafi wuta.

Ta ƙara da cewa, tuni ma’aikatan SEMA sun gudanar da tantance irin ɓarnar da wutar ta yi tare da fara shirye-shiryen samar da kayan agaji.

Manajan KEDCO na yankin Katsina, Aminu Bukari, ya ce; da wuya a samu ƙaruwar wutar lantarki wadda za ta shafi gida ɗaya tak a tsakanin gidaje aƙalla sama da 5,000.

wuta
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

wuta
Labarai

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
wuta
Labarai

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Next Post
An Yi Taron Kara Wa Juna Sani Game Da Hadin-Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Tabbatar Da Tsaro A Kasar Habasha

An Yi Taron Kara Wa Juna Sani Game Da Hadin-Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Tabbatar Da Tsaro A Kasar Habasha

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
wuta

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
wuta

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.